’Yan bindiga sun fasa Jihar Jigawa, sun kashe jami’in tsaro

*Mun fatattake su zuwa cikin daji, inji ACG Abba

Daga Abubakar Muhammad Tahir 

’Yan bindiga ɗauke da muggan makamai sun halaka jami’in shige da fice tare da raunata guda biyu daga cikin jami’an hukumar.

Cikin wata ganawa da manema labarai da Shugaban Hukumar na Jihar Jigawa, ACG Ismail Abba, ya yi da manema labarai a ranar Laraba a Dutse, Babban Birnin Jihar ta Jigawa, ya bayyana cewa, lamarin ya faru ne da misali qarfe 11:20 na dare lokacin da ’yan bindigar suka nufo shingen bincike na hukumar da ke yankin Birniwa-Galadi.

Ya ƙara da cewa, ‘yan bindigar sun zo a babura guda biyu, inda ɗaya daga mashin ɗin yana ɗauke da mutum uku, ɗayan kuma mutum biyu.

“Zuwansu ke wuya suka buɗe wuta kan jami’an hukumar, inda a take ɗaya daga cikin jami’in hukumar mai suna Abdullahi Mohammed (CIA) ya rasa ransa, Abba Musa Kiyawa (DSI) da Zubairu Garba (AII) suka samu munanan raunuka,” inji shi.

Haka kuma ACG Abba ya ƙara da cewa, sakamakon bata-kashi da jami’an nasa, ‘yan bindigar sun jefar da mashinan nasu da wayar hannu ƙirar Tecno T5, suka shiga jeji.

Baburan masu lambar ta Chasis Number MD2A18AXS7MWK81092 da RY157FMINILI2607 ya zuwa yanzu suna hannun jami’an hukumar.

Tuni dai aka garzaya da biyun daga cikin jami’an da suka samu raunka zuwa asibiti, inda kuma jami’in da ya rasa ransa an yi masa jana’iza, kamar yadda addinin Islama ya tanadar.

Daga nan sai kuma ya ƙara da cewa, “na yi farin ciki bisa namijin ƙoƙarin jami’an hukumarmu wajen yin bata-kashi da waɗannan maharan har suka jefar da mashinnansu da wayarsu suka ranta a na kare.

Wannan ya ƙara tabbatar mana, jami’an hukumarmu suna aiki tuƙuru wajen daƙile ayyukan taaddanci.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *