Gwamna Buni zai jagoranci taron Kamfanin Blueprint

*An tsayar da ranar Talata don gudanar da gagarumin taron
*Za a karrama Atiku, Tinubu, Tambuwal, Yahaya Bello da sauransu
*Janar Dambazau zai bajekoli a wajen taron

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A ranar Talata, 16 ga Agusta, 2022, ne Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe zai jagoranci bikin bayar da kyaututtukan yabo na Kamfanin Blueprint, wanda ke buga jaridun Bueprint da Manhaja, inda aka shirya gudanarwa a ɗakin taro na ƙasa da ƙasa ‘International Conference Centre’, da ke Abuja, Babban Birnin Tarayyar Nijeriya.

Babban Jami’in Gudanarwa na Blueprint (COO), Malam Salisu Umar, wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin a wata sanarwa da ya fitar a Abuja, ya ce, ana sa ran Babban Hafsan Sojojin Ƙasa na 17 kuma tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, Laftanar Janar Abdulrahman Bello Dambazau (mai ritaya) zai kasance mai gabatar Babban Jawabi a wajen taron.

Ya ce, Janar Dambazau zai yi magana ne kan ‘Siyasa ta 2023, Tsaron Ƙasa da Zaman Lafiya a Nijeriya.’

Malam Salisu ya ce, an samar da maudu’in ne saboda buƙatar bayar da gudunmawa ga cigaban siyasar qasar da samar da haɗin kan ƙasa.

Ya ƙara da cewa, taron an sadaukar da shi ne, domin lalubo hanyoyin magance ƙalubalen da suka shafi zaɓe, tsaron ƙasa, zaman lafiya da kwanciyar hankali a Nijeriya.

Ya ce, an shirya taron ne, domin karrama manyan ‘yan siyasa da sauran manyan mutane a kamfanoni masu zaman kansu, ɗaiɗaikun mutane da shugabannin ma’aikatu da dai sauransu, waɗanda suka taka rawar gani a wasu fannonin shugabanci da ayyukan jinƙan ɗan Adam.

Wasu daga cikin waɗanda aka zavo domin karramawar a wajen taron sun haɗa da ’yan takarar kujerar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar PDP da Jam’iyyar APC, wato tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, da tsohon Gwamnan Jihar Legas, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu, da sauransu.

Kamfanin Blueprint ya zaɓi mutum biyun ne a matsayin Zaƙaƙuran Dimokuraɗiyya na Shekara a bana yayin taron da aka saba gudanarwa duk shekara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *