Nasiha ga matan da za a yi wa kishiya

Da sunan Allah mai rahma mai jin ƙai, tsira da aminci su tabbata ga shugabanmu Annabin Rahma, Muhammad (SAW).

Ki zama mai mayar da al’amuranki ga sarki Allah, shi ne ya zama gatanki majiɓincin al’amuranki, in ki ka yi haka, kin tsira daga zuwa wajen bokaye da ’yan duba don ƙulla makirci.

Ki kasance mai yarda da ƙaddara domin kuwa tuntuni Allah ya hukunta za ku zauna ƙarƙashin miji ɗaya.

Ki sanya wa ranki cewar mijinki ya yi riƙo ne da sunnar Annabi SAW.

Ki zama mai haƙuri saboda Allah, ba mai haƙurin tilas ba.

Karki takurawa mijinki a kan abubuwan al’ada kamar kayan fadar kishiya da kayan gyaran ɗaki.

Kar ki kuskura ki yarda da zugar ƙawaye, ’yan uwa ko kuma iyaye waɗanda za su umarceki da ki tada hayaniya ga mijinki ko kuma kishiyar taki, ki sani cewa mutuncinki da kimarki za su zube a idanunsu.

Ki ɗauka kishiyarki ’yar uwarki ce abokiyar zamanki ce wajen taimakawa maigidanku yadda zai tafiyar da rayuwa da harkokinsa baki ɗaya.

Ki kasance mai ba ta shawara ta gari wajen sha’anin zamantakewar aure, ku zama masu biyayya ga mijinku matuqar bai saɓa wa umarnin ubangijiba.

Idan kika aikata haka, ya ke ’yar uwata za ki shiga cikin sahun mata na gari waɗanda sakamakonsu shi ne aljanna, Insha Allah.

Gare ki amarya:

Ki zama mai godiya ga Allah da ya kawo ki lokacin aurenki domin baiwa ce ya yi miki wasu suna nan ba su samu ba.

Karki saɓa wa Allah a wajen sha’anin biki, abinda ya kyautu shine ki yi godiya gare shi.

Ki yi taka-tsantsan da shawarar ƙawaye, kar su baki shawarar da za su ɓurmaki domin da yawa akwai maƙiya wanda ba su samu wannan ni’imar da ki ka samu ba.

Ki zama mai yin hanzari a kan abinda mijinki ya ke so.

Ki kula da lokacin da ya ke farinciki, kar kuma ki zama mai baƙin ciki lokacin da ya ke farin ciki ko baƙin ciki.

Duk lokacin da ya zo miki cikin ɓacin rai ko faɗa, to ki zama ruwan sanyi don yayyafa masa wajen kwantar masa da hankali.

Ki yi ƙoƙari ki zauna da ‘ya’yan kishiryaki lafiya ba tare da kin tsangwame su ba.

Ki yi nazarin halayen uwar gidanki hakan zai taimaka miki wajen kyautatuwar zamanku.

Ki guji tava alfarar iyayensa da ’yan uwansa da kuwa abokansa.

Kar ki zama mai yawan kai karar kishiyarki ko talanta gurin mijinku, ki koyi haƙuri da kawaici.

Ki zama mai haƙuri da juriya, kar wani tsanani ya sa ki sauka daga kan abubuwan da aka ɗora ki akai na kyautatawa da biyayya ga mijinki. Idan kikai hakan sai ki zama daga cikin mata na gari wanda za su samu tsira ranar gobe ƙiyama.

Gare ka maigida:

Ya kai ɗan uwa ka tabbatar da cewa za ka ƙara aure ne saboda Allah. Ka zama mai koyi da annanbi yadda ya zauna da iyalansa.

Ka tsaya tsayin daka wajen yin adalci a tsakaninsu.

Ka tsaya wajen koyar da su addini da tsayawa wajen gani imaninsu ya inganta. Sannan ka yi adalci tsakanin ‘ya’yayansu karka fifita wasu daga ciki. Ka yi haƙuri da halayensu domin su masu rauni ne.

Babu wulaƙantacce a wajen Ubangiji sai mai wulaƙanta mata, haka zalika babu mai girma a wajensa sai mai girmama su.

Kuma Annabi SAW ya ce, mafi alkhairinku a cikin mutane shi ne wanda ya fi kyautatawa iyalansa.

Allah ya sa mu dace.

Nafisah Auwal, 08141306201.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *