Muhimmancin zama mutumin kirki

Masu karatu, assalamu alaikum. A wannan makon za mu duba wani sabon maudu’in ne na daban. Wato bayani game da halayyar zama da abokai da ƙawaye. Dalili ke nan ma kanun madu’in namu ya yi tambaya, shin ko kana son zama mutumin kirki a rayuwarka? Ke ma ’yar uwa, ko kina son ki zama mutunniyar kirki a rayuwarki ta duniya?

To ku biyo ni a cikin wannan madu’i, domin ganin matakan da suka kamata mu ɗauka, mu aiwatar a rayuwarmu ta yau da kullum, domin ganin mun cimma matsayin zama na kirki a rayuwa.

A rayuwa, ɗan Adam ba zai iya zama shi kaɗai ba. Idan ma har ya amince ya zauna shi kaɗai ɗin, to ba haka aka so ba, wai ƙanen miji ya fi miji kyau.

Mutum zai iya zama shi kaɗai ne kawai bisa lalura, wacce ba zai iya maganinta ba. Dalili ke nan ya sanya za ka ga mutane na zaune cikin gidaje, a unguwanni, a garuruwa da ƙasashe daban-daban.

Haka kuma ya sanya za ka samu kowane mutum na da abokai, idan mace ce, tana da kawaye. To, wajen zaɓe da zama da abokai da ƙawaye, nan ma akwai abin lura da kula sosai, domin kuwa shi zaɓen da kuma zaman, wani yanayi ne na rayuwa na musamman.

Don haka yana buƙatar a zizara masa sinadari shi ma, domin a samu fa’idar rayuwa, domin a samu rayuwa cikin dacewa da amfani.

Masu iya magana sun ce, abokin damo guza, kamar kuma yadda suka ce, abokin varawo ɓarawo ne. Abin da waɗannan ƙarin maganganu ke nufi a fili su ke, musamman idan mun danganta su da halayyar ɗan Adam ta fuskar rayuwar yau da kullum.

Shi mutum, kamar yadda muka ɗan yi bayani a sama, ba zai iya zama shi kaɗai ba, wannan halayya ce ta sanya kuma ya kasance mai kwaikwayo. A halayya da ɗabi’a, mutum ya kasance mai kwaikwayo, mai rikiɗa kamar hawainiya.

Duk inda ya samu kansa, muddin ya ladabtu da yanayin wurin, to wannan ne zai kasance halayyarsa ta rayuwa. Ke nan duk yanayin irin abokan zamansa ko abokan mu’amalarsa, to irin wannan halayya zai kwaikwaya kuma ta zama ɗabi’a da al’adar rayuwarsa.

Abin buƙata a nan shi ne, mutum ya iya zaɓen abokin zamansa, wanda zai dace da yanayi da rayuwa mai fa’ida ba gurbatacciya ba. Yin haka wani sinadari ne shi ma a rayuwa. Musamman ma idan muka ɗauki ma’anonin waɗannan ƙarin maganganu da muka kawo misalinsu a sama.

Idan ka zamanto Mutumin kirki, mai kyakkyawar manufa a rayuwa, sai Allah ya haɗaka da mutanen kirki masu kyawawan manufofi irin na ka, domin samun cikar burinka.

Koda ka samu matsala da wani daga cikin Jama’arka, kar ka fidda tsammanin alkhairi daga gare shi. Wataƙila idan ka yi masa uzuri ka kyautata zato gare shi, ka yafe masa, sai alkhairi ya biyo bayan hakan.

Mutanen kirki anan duniya, su ne ma’abotan alkhairi a lahira. Kuma mutum ba ya zama mutumin kirki har sai tunaninsa da ayyukansa duk sun zama na kirki.

Ka yi ƙoƙari ka canja rayuwar wani bawan Allah daga mummuna zuwa kyakkyawa. Ko ta hanyar shawarwari, ko taimako, ko agaji, ko kuma ta dalilin afuwarka. Idan ka zamanto Mutumin kirki, mai kyakkyawar manufa a rayuwa, sai Allah ya haɗa ka da mutanen kirki masu kyawawan manufofi irin naka, domin samun cikar burinka.

Allah Ya ba mu dacewa a duniya da lahira, Ilahee Ya Rabbi.

Wassalm. Wasiƙa daga MUSTAPHA MUSA MUHAMMAD, ɗalibi a fannin karatun Injiniyancin Sinadarai (Chemical Engineering) a Jami’ar Federal Polytechnic Kaduna, 09123302968.