Sharhi: Amurka, ki mayar da kuɗin al’ummar Afghanistan

Spread the love

Daga CMG HAUSA

Abdul Sabir dan ƙasar Afghanistan ne da ke rayuwa a birnin Kabul, babban birnin ƙasar, a kwanakin baya, ya je kasuwa don sayo wa yaransa busassun ‘ya’yan itatuwa da riguna domin Ƙaramar Sallah da za a fara nan da wasu kwanaki, amma ya koma gida cikin baƙin ciki, ya ce, “Ban iya sayen kome ba, ko riguna na kasa sayo wa yarana, dukkanin kayayyaki ciki har da busassun ‘ya’yan itatuwa, farashinsu sun wuce ƙarfinmu. Amurka ta ƙaƙaba wa ƙasarmu takunkumi, tare da haramta mu yi amfani da kuɗaɗenmu.”

Alkaluman ƙididdigar da hukumomin ƙasa da ƙasa suka fitar sun nuna cewa, sama da mutane miliyan 23 a Afghanistan na buƙatar agajin abinci cikin gaggawa. Bugu da ƙari, sama da ‘yan Afghanistan miliyan 4 ne suka rasa matsugunansu. Shin alhakin wane ne? Ko shakka babu Amurka ce. A shekara ta 2001, Amurka ta ƙaddamar da yaƙi a Afghanistan bisa dalilin wai “yaki da ta’addanci”. Yaƙin na tsawon shekaru 20 ya yi sanadin mutuwar fararen hula ‘yan Afghanistan 100,000, kuma kusan miliyan 11 sun zama ‘yan gudun hijira.

A watan Agustan shekarar da ta gabata, a ƙoƙarin da take yi na daidaita manyan tsare-tsarenta a duniya, Amurka ta yi gaggawar janye sojojinta daga Afghanistan. A watan Fabrairun wannan shekara, shugaban Amurka ya sanya hannu kan wata doka, da nufin raba kusan dala biliyan 7 na kadarorin Babban Bankin Afghanistan da Amurka ta haramta, zuwa gida biyu, kuma Amurkar za ta yi amfani da rabi don biyan diyya ga waɗanda suka yi hasara a lamarin ranar 11 ga watan Satumba ko kuma harin “9.11”.

Amma ko al’ummar Afghanistan ne suka kai harin “9.11”, har da za a biya hasarar harin da kuɗaɗensu? Biliyoyin daloli ba su da yawa ga Amurka, amma za su iya ceton rayuwar al’ummar ƙasar Afghanistan.

Amurka kullum ta kan ɗauki kanta a matsayin abin koyi wajen kare haƙƙin bil Adam, amma ko ta hakan ne take kare haƙƙin bil Adam?

Mai zane: Mustapha Bulama

By Editor