Sheikh Ibrahim Khalil ya sauya sheƙa zuwa ADC

Fitaccen malamin nan na Kano kuma Shugaban Majalisar Malamai na Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar ‘African Democratic Congress’ (ADC).

Shugaban jam’iyyar ADC na Kano, Musa Shuaibu Ungogo ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai, inda ya ce Sheikh Ibrahim Khalil ya koma ADC ne tare da Dr. Saidu Ahmad Dukawa.

Ungogo ya ce Sheikh Ibrahim Khalil ya sauya sheƙarsa zuwa ADC ne tare da wasu shaihinnan malamai su takwas don ceto Kano daga matsalar rashin jagoranci nagari da barace-barace da kuma shaye-shaye na miyagun ƙwayoyi.

Ya ƙara da cewa, nan ba da daɗewa ba babban ofishin ADC na ƙasa zai shirya gagaumin biki don maraba da Sheikh Ibrahim Khalil da sauransu ya zuwa jam’iyyar.