Sarkin Jama’are, Muhammadu Wabi III ya kwanta dama

Allah Ya yi wa Sarkin Jama’are, Alhaji Ahmad Muhammadu Wabi III rasuwa. Marigyin ya rasu ne bayan fama da rashi lafiya.

Manhaja ta fahimci cewa Sarkin ya rasu ne da tsakar daren ranar Lahadi, bayan da ya shafe shekara 50 a kan sarauta.

Marigayin ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya’ya talatin da biyar.

Sa’ilin da yake sanar da rasuwar sarkin, Gadodamasun Jama’are, Alhaji Salleh Malla ya ce haƙiƙa wannan babban rashi ne ga masarautar Jama’are, jihar Bauchi da ma ƙasa baki ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *