Shekaru 21: Birnin Gwari ba kwanciyar hankali

Idan na ce Birnin Gwari ina nufin ƙasar Birnin Gwari, saƙo da lungunta, ba wai cikin ƙwaryar garin ba cibiyar mulki da hada-hadar kasuwanci.

Ƙasar Birnin Gwari mai faɗin murabba’i sama da Dubu Shida, ƙasa ce ta manoma. Zaman lafiya da kwanciyar hankali da son jama’a musamman baƙi, su ne halayen nagarta da aka san ƙasar Birnin Gwari tun kafin Jihadin Mujaddadi Shehu Ɗan Fodiyo.

Tarihi ya tabbatar da cewa, akwai Musulunci a ƙasar Birnin Gwari mai inganci kuma mai ƙarfi tun kafin Mujaddadi Shehu Ɗan Fodiyo ya tsaida jihadi a kan ƙasar Hausa. Wannan ne ma yasa Shehu Ɗan Fodiyo bai yaƙi ƙasar Birnin Gwari ba, sai dai ya ajiye wakilinsa, wanda a yau yake ɗaya daga cikin ‘King Makers’ a masarautar Birnin Gwari.

An tabbatar da cewa Abdullahin Gwandu da Sarkin Musulmi Muhammad Bello duk sun yi tattaki zuwa ƙasar Birnin Gwari. Kodayake tarihin kan zo da mabambamtan ra’ayi.

Bayan jihadin Shehu, tarihi ya nuna cewa an samu wani Ɗan Sarki da yake da jiɓi da gidan Mujaddadi wanda ya cutar da ƙasar Birnin Gwari ta hanyar yi mata ƙawanya ta kowacce kusurwa tsawon watanni, ba da nufin jihadin Musulunci ba, sai domin faɗaɗa ƙasar mulki. Haka aka kwashe tsawon watanni ba shiga ba fita. Yunwa ta durfafi al’umma wanda a sakamakon haka aka ƙaƙaba wa ƙasar Birnin Gwari wani tarihi wanda bai dace da jarumtar mayaƙanta ba.

Ba a taɓa samun lokacin da al’ummar ƙasar Birnin Gwari suka shiga kunci da damuwa ba irin wancan lokacin, shekaru 200 baya. Yaƙi ne amma ba gaba da gaba ba, samfurin karya tattalin arziki da ƙaƙaba yunwa ga al’umma. Wasu masana tarihi na ganin cewa tun wancan lokacin, watau shekaru kamar 200 da suka gbayanabata, ƙasar Birnin Gwari ba ta shiga halin ƙunci da koma tattalin arziki ba sai cikin shekatu 21 zuwa yau.

Rayuwar al’umma ta ci gaba da wanzuwa cikin nishaɗi da raha da walwala tsawon shekaru 170 baya a ƙasar Birnin Gwari. A cikin waɗannan shekarun ne sarakunan ƙasar waɗanda suka yo gadon Musulunci tun zamanin Umar Sheriff, suka sake gina ƙasar tare da kafa ta a doron koyarwar addinin Musulunci har abada. Wannan ya tsole wa maƙiyan ƙasar Birnin Gwari ido sosai.

Sarakuna da Malamai Waliyyai da aka yi a ƙasar Birnin Gwari su ne suka kafe garin da adduoin tsari.

A da, kura ba ta iya ratsa garin saboda tsarkin zuciyar al’ummar Birnin Gwari. Tarihi ma ya tabbatar da cewa duk wani mutum mugu da ya ratsa ta ƙasar Birnin Gwari a wancan zamanin, to asirinsa zai tonu, kuma ƙarshen sa yazo kenan. Wannan kyakkyawan tarihin ya kau, domin al’umma sun canza daga bin Allah zallah, abinda ya hana Mujaddadi tsaida jihadi a kan ƙasar Birnin Gwari, zuwa aikata sabon Allah da zuwa da miyagun halaye. Wannan kuwa duk da cewa Sarkin Birnin Gwari yana a tsaye tsayin daka kullum wajen gyara da tsarkake zukatan al’ummarsa ne. Ba a taɓa yin Sarki mai ƙoƙarinsa ba. Ƙoƙarin nasa ya sa Allah ke duban mu da rahama har aka samu ƙasar ta cigaba da wanzuwa har zuwa yau. In da yadda wasu miyagun ke so ne, wataƙila da yanzu ƙasar ta fashe, ta watse kuma ta tsiyaye, kamar dai yadda aka taɓa yi a zamanin baya.

Tun bayan Gwamnan Soji, Kanal Hamid Ali, wanda ya nuna wa ƙasar Birnin Gwari so da ƙauna na zahiri, sauran gwamnonin da aka yi, sai dai su kwatanta kawai.

A yau, ƙasar Birnin Gwari ba ta da wani muradi da ya wuce kawo ƙarshen bala’in da ya afka mana shekaru Ashirin da Ɗaya da Suka gabata zuwa yau. Bala’in “Yan fashi da makami, bala’in bandits.”

Wataƙila, idan mun gyara halayenmu zuwa irin halayen Musulunci, muka so juna, muka kauce wa rarrabuwar kai, ƙila a lokacin mu samu sararawa.

Ƙasar Birnin Gwari ƙasar Musulunci ce gaba da baya! Abinda duk ya gyara al’ummar ƙasar Birnin Gwari a shekaru 170 da aka kwashe cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali da bunƙasar tattalin arziki, shi zai gyara mana al’ummar yanzu ya kuma taimaka mana wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da aminci. Duk abinda bai kasance hanyar arzikin wancan al’ummar da ta gabace mu ba, mu ma ba zai kasance haryar arzikinmu ba. Allah Ya sa mu dace.

Isa Muhammad Galadima shi ne Sakataren Haɓaka cigaban Ƙasar Birnin-Gwari