Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Kowacce ranar ɗaya ga watan Oktoba tana zuwa wa ‘yan Nijeriya a matsayin rana ta musamman, ranar nuna farinciki da jindaɗi, saboda murna da samun ’yancin kai da Nijeriya ta samu daga turawan mulkin mallaka na ƙasar Ingila. Bayan gwagwarmaya da faɗi tashin da kakaninmu na baya suka yi wajen tabbatar da ganin al’ummar ƙasar nan sun samu ’yancin gudanar da mulkin kansu da tafiyar da harkokin siyasar ƙasarsu da kansu.
Ba za a ce an samu ‘yancin cikin sauƙi ba, don mulkin mallaka, kamar yadda sunan ya nuna, mulki ne na nuna ƙarfin iko da zalunci da danniya. Ba ku da damar juya tattalin arziƙinku da kanku, kuma komai naku sai kun nemi izini kafin a amince muku cikin sharuɗɗa masu tsauri. Ba ku da damar shiga takarar neman muƙamin siyasa ko riƙe wani matsayi na mulki, sai bisa tsarin da ‘yan mulkin mallaka suka yarje muku.
Nijeriya ta samu ‘yancin kanta ne cikin ruwan sanyi ba tare da zubar da jini ba, wannan ya nuna irin wayewa da kyakkyawan jagoranci da shugabannin gwagwarmayar neman ‘yancin kai suka nuna a wancan lokacin. Shugabanni irin su Herbert Macaulay, Obafemi Awolowo, Nnamdi Azikiwe, Abubakar Tafawa ɓalewa, Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato, sun taka muhimmiyar rawa wajen ganin Nijeriya ta samu ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka. Ta hanyar rubuce-rubuce a jaridu, da gwagwarmayar ƙungiyoyin ma’aikata, da na ’yan siyasa irinsu Akintola da Malam Aminu Kano. Haka nan marubuta da mawaƙa irinsu Malam Abubakar Imam da Malam Sa’adu Zungur, da Malam Abubakar Ladan Zariya, sun tayar wa da turawa hankali da irin basira da fasahohin da Allah ya basu. Wannan ya taimaka wajen samar wa ‘yan Nijeriya ‘yancin kai a siyasance da harkokin tattalin arziƙi da zamantakewa.
Shekarar 1960 ta kasance shekarar da ƙasashen Afirka da dama suka samu ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka. ƙasashe irinsu Kamaru, Togo, Mali, Senegal, Iɓory Coast da Cadi, da suka karɓi ’yancin kansu daga turawan ƙasar Faransa. Da ƙasar Congo, Somaliya da Nijeriya, duk sun samu ‘yancin kansu ne a shekarar 1960.
Samun ‘yancin kai a wancan lokacin abu ne na farinciki ga ɗaukacin al’ummar ƙasar nan, duk da kasancewar ba kowa ne ya yi maraba da haɗin gambizar gabashi, kudanci, da arewaci da aka yi wa ƙasar da sunan haɗaɗɗiyar Nijeriya ba. Kuma a dalilin haka ne har kawo yanzu shekaru 64 da samun ’yancin kai ake cigaba da samun ƙalubale iri-iri, da ke barazana ga cigaba da kasancewar ƙasar a dunƙule a matsayin ƙasa ɗaya.
Tarihin Nijeriya ba zai manta da Yaƙin Basasa da ƙasar ta fuskanta ba a lokacin da ‘yan awaren yankin Biyafira, daga ɓangaren Kudu-Maso-Gabashin ƙasar nan, suka ayyana ɓallewa daga haɗin gambizar Nijeriya ba, wanda sanadiyyar haka aka samu asarar ɗimbin rayuka da dukiyoyi daga kowanne ɓangare, har ta kai ga dakarun gwamnatin Nijeriya suka samu galaba akan ’yan tawaye.
Haka kuma wannan matsala ta cigaba da tasowa lokaci zuwa lokaci, musamman daga yankin Inyamirai ’yan ƙabilar Ibo, da kuma yankin ƙabilar Yarabawa dake shiyyar yammacin ƙasa, inda wani ɗan kishin yarabanci Sunday Igboho yake jagorantar wata ƙungiya mai ragin ware yankin Yarabawa daga Nijeriya, don kafa ƙasar su ta kansu. Za a iya cewa yankin Arewa ne kaɗai bai samu irin wannan gangami da turjiya ta ‘yan aware ba, in ban da ƙananan ƙungiyoyi na ’yan bindiga masu aikata laifuka, da fashi da makami.
A duk lokacin da aka ce shekara ta zago, ana shirye-shiryen bikin Ranar Samun ‘Yancin Kai, akan ga yadda ‘yan Nijeriya ke ta shirye-shirye da tsara abubuwan biki iri daban-daban, irinsu buga riguna na musamman, buga tutoci, da tarukan bukukuwa don murna da wannan biki. Amma a ‘yan shekarun baya-bayan nan an ga canji sosai, saboda yadda matasa suka yi biris da bikin zagayowar ranar, domin nuna damuwarsu da yadda tattalin ƙasar nan ke fuskantar koma-baya, da halin ƙuncin rayuwa da ‘yan ƙasa ke daɗa shiga. Suna ganin babu wani abu da za a yi wa murna, sakamakon yadda ƙasar ke daɗa canzawa daga asalin yadda a baya aka yi zaton samun ’yancin kai zai kawo wa ƙasar nan bunƙasa da cigaba. Abin takaici da mamaki sai gashi kullum abubuwa sai baya suke daɗa yi, har wasu na ganin gwamma jiya da yau.
A lokacin da Nijeriya ke ƙarƙashin mulkin mallaka, akwai ayyukan raya ƙasa, ingantattun hanyoyi, kiwon lafiya, ilimi, da masana’antu, da kuma kyakkyawan tsarin shugabanci da yake duba maslaha da jindaɗin talakawan ƙasa. Amma yanzu da aka samu damar faɗaɗa shugabanci da bunƙasar tattalin arziƙi, da ƙaruwar hanyoyin shigar kuɗaɗe, a maimakon a ga a cigaba da bunƙasa, sai abubuwa ne ke ƙara taɓarɓarewa, cin hanci da rashawa na ƙaruwa, shugabanni na cin amanar talakawa, ga zalunci da danniya a sha’anin mulki da rayuwa, wanda a kullum sai daɗa bayyana yake yi.
Musa Balarabe Musa, wani marubuci ɗan Nijeriya, kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, ya bayyana cewa, ‘Dimukraɗiyyar da yanzu muke yi wacce ya kamata ta kawo wa talakawa sauyi mai ma’ana da cigaban rayuwa ta zama makamin da ’yan siyasa ke amfani da ita wajen ƙara arzuta kansu da jefa talakawan ƙasa cikin yunwa da talauci.’
Wani marubucin tarihi, Basil Daɓidson, ya taɓa rubutawa cikin littafinsa mai taken, ‘The Struggle for Africa’s Independence’ cewa, ‘Samun ‘yancin kai bai taɓa zama cikar buri ba, sai dai ya zama masomin samun samun ingantacciyar rayuwa ga ‘yan ƙasa.’ Ya kamata ‘yancin kan Nijeriya ya zama ginshiƙin gina ingantacciyar ƙasa, bunƙasar tattalin arziƙi, samar da shugabanci nagari, da tabbatar da adalci ga kowa. Ba kamar yadda a yanzu muke gani yana faruwa, daga irin ’yan siyasa da ‘yan bokon da suke jagorancin ƙasar nan ba.
A saƙonsa na zagayowar Ranar Samun ‘Yancin Kai, Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar wa ’yan Nijeriya ƙudirin gwamnatinsa na samar da mafita mai ɗorewa domin rage musu raɗaɗin matsin rayuwa da suke ciki, ƙarfafa haɗin kan ƙasa, da samar da ayyukan yi ga matasa. Ya ce, ‘Ina sane da halin ƙunci da dayawa daga cikin ku ke fuskanta a cikin waɗannan lokuta masu ƙalubale. Gwamnatinmu ta san cewa yawancinku suna fama da tsadar rayuwa da neman aiki mai tsoka. Ina so in tabbatar muku cewa ina jin koken ku,’ kamar yadda ya faɗa.
Sai dai anya ‘yan Nijeriya za su saurari uzurin shugaban ƙasa a wannan lokaci da a kowacce rana rayuwa ke ƙara tsananta a wajensu, kuma suna ji ana ware maƙudan kuɗaɗe ana bai wa gwamnoni don sauƙaƙawa talakawa, amma babu wani abin a zo a gani da ake yi a zahiri sai dogon Turanci. A lokacin da ake cewa, tattalin arziƙin ƙasa na fuskantar ƙalubale a lokacin ne kuma ake zargin fadar shugaban ƙasa da batun sayen jirgin shugaban ƙasa, jirgin ruwan iyalin shugaban ƙasa, da motoci masu sulke da albarushi ba ya ratsawa. Abubuwa da dama da suke faruwa na ƙara nuna gazawar hukumomi da masu riƙe da madafun iko kan abubuwan da suke cewa suna yi don inganta ƙasa da abin da ake gani suna yi su da iyalinsu a zahiri.
A jawabinsa na Ranar Samun ‘Yancin Kai, Shugaban ƙungiyar Kare Haƙƙoƙin Musulmi ta MURIC a Nijeriya, Farfesa Ishaƙ Akintola ya buƙaci ’yan Nijeriya su karkatar da dubansu zuwa ga gwamnoni da wakilansu a matakin jihohi saboda mafiyawan lokaci rijiya na ba da ruwa guga na hanawa ne. Daga sama Gwamnatin Tarayya tana ware wasu kuɗaɗe ko tsare-tsaren da talakawa za su samu sauƙin rayuwa, amma a ƙasa kuma wasu jami’an gwamnati masu kwaɗayi da son zuciya suna karkatar da su zuwa ga kasuwanni don sayarwa, ko rumbunan su don cin kasuwar siyasa idan lokacin yaƙin neman zaɓe ya gabato.
