Shekaru biyar za a kwashe a jere ana fama da tsananin zafi- Bincike

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa, tun daga shekarar da muke ciki ta 2023 zuwa 2027 za su kasance masu tsananin zafi da ba a taɓa samu ba a tarihi, sakamakon yadda tiriri mai gurɓata muhalli ke ci gaba da yawaita.

Ƙwararrun majalisar kan yanayi sun bayyana cewa, duniya za ta ga shekaru biyar a jere da za a yi tsananin zafi wanda ke da nasaba da ɗumamar yanayi da ke ci gaba da barazana ga halittun ban ƙasa.

Bayan wani taro da tawagar ƙwararrun ta gudanar, biyo bayan dogon bincike game da tsananin zafin da duniya ke gani, sun ce cikin shekaru biyar masu zuwa akwai hasashen yiwuwar a iya samun shekara guda marar tsananin zafi.

Kafin wannan bincike na ƙwararrun dai shekarar 2015 zuwa 2022 su ne ke matsayin shekaru mafiya tsananin zafi da duniya ta gani, yayinda zafin na wannan karon ke ƙoƙarin zarce wanda aka gani a waɗancan shekaru.

A cewar ƙwararrun shekara bayan shekara tsananin zafin zai ci gaba da ruvanya wa matuƙar ba a sauki matakan da suka kamata wajen rage fitar da tiriri mai guba da manyan ƙasashe masu masana’antu ke yi ba.

Yarjejeniyar yanayi ta birnin Paris a shekarar 2015 da ƙasashe da dama suka sanyawa hannu dai ta amince da rage tiririn da ake fitarwa zuwa aƙalla 1850 ko 1900 ta yadda yanayin ba zai haura maki 1.5 a ma’aunin yanayi na Celcius ba amma kuma ƙasashe suka gaza mutunta yarjejeniyar.