Mu na cigiyar masu yi wa gwamnatin Ganduje kwarmato – NNPP

Daga RABI’U SANUSI Kano

An buƙaci al’ummar Jihar Kano da su taimaka wa gwamnati mai jiran gado a ƙarƙashin jagorancin Abba Kabir Yusif da bayanai kan yadda aka gudanar gwamnati mai barin gado a jihar a ƙarƙashin jagorancin Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Wannan na zuwa ne daga bakin shugaban kwamitin karɓar mulki na gwamnan Kano mai jiran gado, Dr. Baffa Bichi, inda ya buƙaci al’ummar jihar Kano da su taimaka wa gwamnati mai mai zuwa da bayanai game da gwamnatin Abdullahi Ganduje.

Dr Baffa Bichi ya bayyana haka ta hannu babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan mai gado Malam Sanusi Bature Dawakin Tofa a ranar Laraba.

Sanarwar ta nemi duk wanda ke da wasu muhimman bayanai kan yadda aka gudanar da gwamnatin Kano daga shekarar 2015 zuwa 2023, zai Iya mika bayanan shalkwatar kwamitin karɓar mulkin dake Tahir Guest Palace, lamba. 4 kan titin Ibrahim Natsugunne.

“Haka kuma zai iya aike da bayanan ta wannan adireshin gmail: [email protected],” a cewar sanarwar.

Idan za a iya tunawa, wannan na zuwa ne yayin da ya rage kwanaki 11 a rantsar da sabuwar gwamnati a Kano da matakin ƙasa baki ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *