Daga USMAN KAROFI
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya isa Davos, Switzerland, domin wakiltar Nijeriya a taron shekara-shekara na 2025 na taron tattalin arziƙi na duniya (WEF). Taron na bana ya haɗa shugabanni daga sassa daban-daban na duniya, manyan ‘yan kasuwa, da abokan cigaba domin tattaunawa kan manyan ƙalubale da damammaki a fannin tattalin arziƙi.
A cikin jadawalin ayyukan sa, mataimakin shugaban Ƙasa zai halarci tarurruka masu muhimmanci, ciki har da wani taro mai taken “Taswirar samar da damammakin zuba jari ga kasuwannin Afirka,” wanda bankin ci gaban Afirka (AfDB) ya shirya tare da haɗin gwiwar WEF. Wannan taron zai mayar da hankali kan jawo jarin ƙasashen waje zuwa Afirka don tallafawa ci gaba mai ɗorewa da ƙarfafa nahiyar.
Haka zalika, Shettima zai ƙaddamar da wani muhimmin shiri mai suna “Taswirar zuba jari don Tallafawa jin ƙai shiyyar Afirka*, wanda aka tsara tare da haɗin gwiwar AfDB da abokan hulɗar ci gaba. Har ila yau, zai jagoranci wani zama mai taken “Mai da cinikin Dijital wata maɓalli ga ci gaban Afirka,” inda za a tattauna hanyoyin hanzarta amfani da yarjejeniyar Cinikin Dijital ta AfCFTA.
Daga cikin sauran ayyukan sa, mataimakin shugaban Ƙasa zai halarci bikin bayar da kyaututtuka na Crystal Awards na 2025, sannan kuma zai kasance ɗan tattaunawa a wani taro mai taken “Haɗurran Duniya na 2025,” wanda zai nazarci manyan haɗurran siyasa, fasaha, da muhalli da ke shafar duniya.
Mataimakin Shugaban Ƙasa ya tafi Davos tare da tawagar gwamnati wadda ta haɗa da ministan masana’antu, ciniki da zuba hari, Dr. Jumoke Oduwole, da sakataren hukumar ɓunƙasa jarin Nijeriya (NIPC), Aisha Rimi. Ana sa ran zai koma Abuja bayan kammala aikace-aikacen sa.