Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Wannan tambaya ce mai muhimmanci idan mu ka duba lamarin tsaro ya shafi kowa kuma son samu kar a cusa siyasa, kabila ko wani son kai har dai za a tinkari ƙalubalen a kuma samu maslaha. Najeriya na daga cikin kasashen duniya da ke fama da matsalar tsaro.Tun a na maganar ‘yan OPC a kudu maso yamma da masu rajin kafa ƙasar Oduduwa, zuwa tsagerun Neja Delta masu fasa bututun fetur da sace Turawa zuwa ‘yan ta’addan IPOB da su ka ce lallai sun sun cimma burin kafa ƙasar Biyafara don haka su ka shiga kashe duk wanda ba sa kauna. Mu duba yadda Lardin Arewa ya yi fama da fitinar maitatsine masu yanka mutane yankan rago, boko haram su ka ɓullo da fakewa da addini su na kai hari dakunan ibada har kuma satar shanu a Arewa maso yamma ta juye zuwa ‘yan ta’adda masu satar mutane don karɓar kuɗin fansa su ka bunkasa har garuruwa su ke sanyawa haraji. Mutanen da abun kan shafa ba manya balle yara, ba mata ko tsoffi kowa kaddara kan iya fadawa kan sa. Mun sani fitina ta na da illa ainun don in ta tashi za ta iya shafar wanda ba ruwansa. Nijeriya mai mabiya addinai da kabilu da al’adu daban-daban kuma ƙasar baƙar fata mafi yawan mutane a duniya na zama abar sharhi a duniya don kuwa in fitina ta shafi Nijeriya ta kan iya tasiri kan ƙasashe makwabta da zama darasi a siyasar duniya. Shin masu hankali za su zuba ido su na gani har sai fitina ta zo har cikin ɗakinsu sannan su arce? Hakki ya rataya kan kowa ya ba da tasa gudunmawa don samun sauƙi. Wani ya yi da baki wani kuma musamman mai madafun iko ya yi amfani da hannun sa. Ba abun da ya fi riba irin zaman lafiya a kasa. Shin addini ne, kasuwanci ne, noma da kiwo da duk wasu lamuran yau da kullum na buƙatar tsaro don gudanar da su cikin natsuwa da nasara.
Bai zama wani sabon abu ba idan mutum ya yi rubutu kan muguwar illar masu farafagandar kwangilar rusa Arewa ta kururuta wutar ƙabilanci; sai wani dan kwangila ƙarami ko babba ya yi caraf ya kawar da kai kan sakon sai ya yi martani “me ya sa ba za ka yi magana kan ‘yan ta’adda masu kashe mutane a daji ba…in da a kan ‘yan ta’adda ka maida hankali kan wannan rubutun da yanzu an gama das u” maganganu ne da na takaita da ‘yan kwangilar su ka haddace. Sau tari kuma su kan jefi masu yaƙi da ƙabilanci da cewa agwai ne yanda kananan kabilun Arewa ta tsakiya ke zaiyana Fulani musamman na daji. Kalmar agwai na nufin mutum marar wayo daga yadda asalin wasu Hausawa masu zolayar Fulani ke kiran Fulanin daji wato gailo. Gailo na nufin wawan mutum. Don haka duk wanda ya ce agwai za ka gano daga Arewa ta tsakiya ya ke tsakanin jihar Kaduna, Filato zuwa Taraba da ma Binuwai. Matar nan mai yayata sharri na kunna fitinar ƙabilanci har ma ta kan kara da “ribar tallar nono” ga wanda ta ke son muzantawa hatta cikin mutanen ta da kamar wasan kwaikwayo su ka samu sabanin hanyar aiwatar da kwangilar ta ganin Musulmin Arewa sun hargitse da yaki a tsakanin su a yi ta kisan kan mai uwa da wabi. Bincike ya gano cewa hatta barayin dajin ma an yi amfani da su wajen tada fitina don samun hanyar ƙirƙiro ‘yan kwangilar da za su fake da su wajen kunna babbar fitinar.
A tarihin annamiman duniya dama haka su ke aikatawa. In ban da kalilan, akasarin ƙungiyoyin ta’addanci ƙirƙiro su a ka yi don cimma manufar rusa wata al’umma, al’ummar kai tsaye MUSULMI. Addinin musulunci ya gagari tunanin fasikan duniya don ya na hannun riga daga manufofin su da tsarin rayuwar su ta shan giya, fantamawa, taron rawa da waka irin wanda a ka yi a Isra’ila na Noɓa a ranar 7 ga Oktoba 2023 har ‘yan Hamas su ka kutsa da wasu laimomi masu farfela su ka wargaza taron; da hakan ya haifar da wannan fitinar ta Gaza shekaru 7 kenan a ka kashe fiye da Falasɗinawa 62,000.
Wallahi sai dai masharranci ya ki Allah ko kuma dama in ba na Allah ba ne ba mamaki, amma mutum ya ce ba a magana da kira da babbar murya a kawo ƙarshen fitinar ɓarayin daji ba gaskiya ba ne sam-sam. Asalin al’ummar Arewa maso yamma sun san yadda lamarin ya fara kuma wasu ma sun san gaggan matasan da a ka yi amfani da su, su ka zama ‘yan ta’adda. Wanda yanzu a ka fi ambata Bello Turji ai ba shi ne babban madugun ba. Da yawa ba su san labarin Buharin daji ba, Dogo Gide, Halliru sububu, Baleri, Boderi, Kachalla Ali da sauran su. An samu nasarar gamawa da miyagun barayin wasu ma faɗa su ke yi su hallaka juna. Ga Lakurawa daga ƙetare.
Malaman addini, masu sharhi a kafafen labaru da sarakunan gargajiya sun yi magana har bakin su ya gaji amma fitinar ba ta kwanta ba. Wani lokacin a kan samu nasara. In don sheƙe ɓarayin ne da magana a kan su zai sa su kare wallahi da sun kare. Ni dai ban san adadin hirarrakin da na ɗauka na kira ga yaki da ɓarayin ba. Wato a na fara fitowa daga fitinar Boko Haram a yankunan mu na Arewa maso gabar sai wannan fitina ta fara daga satar shanu ko bisashe kamar yanda al’ummar Arewa maso yamma ke faɗa. Akwai wasun mu har tsallake rijiya da baya mu ka yi daga sata ko kashewa na ɓarayin daji. Don haka wanda ka ji ya ce ba ma magana a kan su bai ma na adalci ba ko dama bai ma san mu ba sam. Idan dan bana bakwai ya ce ba a magana kan ɓarayin daji ai sai dai a ƙyale shi don yaranta dangin hauka.
A fili ya ke masu tattara Fulani kakaf su shafa mu su bakin fenti da cewa duk ‘yan ta’adda ne, kwangila a ka ba su don haddasa yakin ‘yar gaba daya a tsakanin dangin juna na arewacin Arewa. Miyagun duniya sun fahimci da Hausa a ke wa’azi a ƙarfafa addinin Musulunci, don haka su ka kirkiro wasu mutane da ba Hausawa ba, su ka ɗau nauyin su wajen bude shafuka a yanar gizo don kunna wannan wutar. Yanda na ga wasu da a ka yaudara na ɗaukar caji akwai damuwa in an kawar da ido daga kan wannan farafagandar. Abun nan ya zama sana’a da wasu matasa ke samun kuɗin shiga shi ya sa in mutum ya kawo batun taka mu su birki sai su yi ta antayo bakaken maganganu don mutum ya gaji ya kyale su, su cigaba da samun albashin su. Yo albashi ta tada fitina ai haramtacce ne marar albarka.
Hatta ƙungiyar makiyaya ta Miyetti Allah wacce tamkar ƙungiyar mahautace ta Hausawa na nuna damuwa kan barayin na daji don su kan rutsa da makiyayan da ba ruwan su. Akwai ma’abota shanu da yawa da su ka zama cikin tsaka mai wuya, ba sa samun aminci daga mutanen gari ba sa samun sauki daga jami’an tsaro kuma ba sa samu daga barayin daji. An kashe da yawa daga cikin su amma labarin ba ya fitowa don a daji su ke. Haka ya sa wasu malamai a Arewa maso yamma faɗakarwa kan illar rashin bincike wajen ɗaukar matakin mutan gari kan makiyaya. Haƙiƙa Fulanin daji na da kamanni irin na daji kuma ko ba miyagu ba ne za su iya fadawa tarkon a danne su a kasuwa a yanka kuma magana ta kare don a kan yi hakan da sunan yaki da ɓarayin daji. Har yau mataimakin shugaban ƙungiyar Miyetti Allah na ƙasa Atiku Modibbo daga Katsina ba a san inda ya ke ba kimanin shekaru uku da su ka wuce. Modibbo darakta ne ma a jihar Katsina. iyalin sa sun yi kuka har hawayen su ya kafe. A na tsammanin an sace shi kan hanyar Kaduna zuwa Abuja kuma ta yiwu ya na lahira. Baba Usman Ngelzarma daga jihar Yobe shi ne shugaban ƙungiyar makiyaya ta Miyetti Allah CATTLE BREEDERS ASSOCIATION MACBAN yayin da Bello Bodejo a ofishin sa da ke jihar Nasarawa ke jagorantar Miyetti Allah kautar hore mai kasuwar shanu ta Maliya. Wasu ba sa ma tantance bambancin kungiyoyin biyu kawai Miyetti Allah Miyetti Allah kawai ya kama bakin su!
KAMMALAWA
Jama’a duk mai tunani ya san yanzu lokaci ne na aiki tukuru wajen yaki da fitinar kunna wutar ƙabilanci wacce sau 100 ta fi sharrin barayin daji da a ke magana. Duk wanda bai san gari ba ya saurari daka, faɗan ƙare dangi na Rwanda tsakanin Hutu da Tutsi ya isa misali. Bayan an kusa kashe kowa ‘yan sauran da su ka rage su ka shiga tattaunawa. Allah ya kiyaye mu daga faɗawa har halin tattaunawa. Mu tashi tsaye don kashe wannan fitinar a yanzu. Na hango hannayen maƙiya Arewa a wannan fitinar kuma aƙalla na fara haska su.
