(Ci gaba daga makon jiya)
Daga AISHA ASAS
Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Iyali na jaridar al’umma ta Blueprint Manhaja.
Allah Ya albarkace iyalanmu, Ya hore mana abin buƙatun yau da kullum.
Idan ba kuma manta ba, kuma kuna biye da mu, mun fara wannan darasi da shimfiɗa kan yadda aka ɗauki ƙayyade iyali a ƙasar Hausa, da yadda aka yi kuɗin goro kan duk wani abu da ya shafi ƙayyade iyali.
Mun kuma kawo yadda iyaye suka gwamace yawan aure-aure da haifawa titi yara, da su yi bincike a Musulunce ko akwai inda ya halasta a ƙayyade iyali da kuma yadda addini ya sanar za a yi shi.
Saidai abin mamaki a shekarar 2023 zuwa wannan shekara ta 2024 da muke ciki, an samu raguwar yawan haihuwa, wanda rahotanni suka nuna wayewar kai da kuma aminta da shirin ƙayyade iyali da aka jima ana masu talla.
Rahoton ya bayyana cewa yawan haihuwa ga samari ya yi ƙasa inda ake samun haihuwa 77 a cikin mata 1,000 masu shekaru 15 zuwa shekaru 19, amma tana ƙaruwa sosai yayin da suke ƙara shekaru, inda ake samun haihuwa 233 a cikin mata 1,000 da shekarunsu suka kai 25 zuwa 29.
Rahoton ya ƙara nuna bambance-bambance da ake samu a matakin jiha, inda a Birin Tarayya Abuja ke da yawan haihuwa na 3.2, yayin da aka samu 2.9 a Jihar Riɓers. Ita kima Yobe wadda ke da mafi yawan yara da 7.5 kowacce mace.
Kamar yadda rahoton NDHS ya bayyana, waɗannan alƙaluma na iya tasiri ta hanyar zamantakewa da kuma al’adu.
Binciken ya nuna mahimmancin samar da shirye-shiryen kiwon lafiyar haihuwa.
ƙwararru a fannin kiwon lafiya sun buƙaci gwamnati da ƙungiyoyi masu zaman kansu da su ƙara ƙaimi wajen samar da ayyukan kiwon lafiya da suka jiɓinci haihuwa, musamman a yankunan karkara da jihohin da muke da su.
Yayin da yawan al’ummar Najeriya ke ci gaba da ƙaruwa, masana sun yi nuni da cewa, inganta samar da kayan aikin kiwon lafiya na haihuwa da tsarin iyali na da matuƙar muhimmanci domin tabbatar da ci gaba mai ɗorewa, da kwanciyar hankali da kuma inganta rayuwa.
Dakta Jane Dasat, wata ƙwararriyar kan sha’anin kula da lafiyar mata masu juna biyu, ta bayyana cewa saka hannun jari a ayyukan ƙayyade iyali na ɗaya daga cikin dabarun rage mace-macen mata masu juna biyu.
Dasat ya ce “Lokacin da mata suka sami damar yin rigakafin hana haihuwa kuma za su iya tsara yadda za su ɗauki juna biyu, ba za su iya fuskantar matsalolin da ke haifar da mutuwar mata masu juna biyu ba.”