Shin majalisa ta 10 za ta iya gocewa jama’ar Shata?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Batun da a ke yi a ’yan kwanakin nan shi ne na mara baya ga waɗanda za su jagoranci majalisar dokokin Nijeriya ta 10. Tun fara dimokraɗiyya a Nijeriya daga samun ’yanci a 1960 an samu Majalisun Dokoki guda tara ne inda yanzu a ke shirin rantsar da ta goma. A cikin majalisun nan an samu shugabannin majalisa kusan ninkin yawan majalisun don dalilan da kan sa a tsige shugaban majalisa.

A ’yan shekarun nan lamarin ya yi sauƙi don har ma daga 1999 zuwa yanzu an samu Shugaban Majalisar Dattawa guda ɗaya da ya yi wa’adi biyu kan karaga da hakan ya sa daga bisani duk da ya na cikin majalisa sai ya zama ba ya wani tasiri tun da tamkar ya ƙure muƙamin majalisa inda ya dawo memba a majalisar ta dattawa. David Mark kenan daga Jihar Binuwai wanda tabbas masu karanta wannan shafi na ALƘIBLA a wannan mako za ku amince da ni cewa an ma daina jin duriyar David Mark.

A kwanakin baya ma abun da ya sa sunan sa ya fito kafafen labaru shi ne mutuwar dan sa don haka manyan lasa su ka riƙa aika ma sa ta’aziyya. Duk yadda shugaban Majalisar Dattawa ko kakakin wakilai ya daɗe kan kujera matuƙar bai yi wani tasiri na tsayin daka kan hana ba daidai ba, to ya na wucewa zai yi wuya a riƙa tunawa da shi. Hakan kuwa ba ya na nuna ina nufin Mark bai taɓuka komai ba ne.

Tsoffi da sabbin ‘yan majalisar dokokin Nijeriya sun tare a Abuja don mara baya ga waɗanda su ke son su jagoranci majalisar ta 10 da za ta fara aiki a watan gobe.

A wannan karo hatta tsoffin ‘yan majalisar da ba sa kan gadon wakilici ke sa baki a mara baya ga ‘yan takara. Hakan na nuna neman cimma muradu na siyasa ba tare da lalle biyewa buƙatun wata jam’iyya ba. Kazalika yadda ’yan takarar ke da yawa ko kuma wasu ke son cankar ’yan takarar waje da tsarin rabon muƙamai da ’yan jam’iyya ke yi don samun haɗin kai daga shiyoyin siyasa 6 na Nijeriya.

Wannan na faruwa duk da jam’iyyar APC ta canki waxanda ta ke son su samu muaman yayin da shi ma zaɓaɓɓen Shugaba Tinubu ke da ra’ayin da ba ya nesa daga na APC. Gaskiya ma APC na aiki ne da Tinubu don al’adar jam’iyya mai mulki ne a Nijeriya bin ra’ayin shugaban qasa ko da hakan bai zo daidai da ra’ayin wasu daga shugabannin jam’iyya ba don yadda shugaban ƙasa ke da ƙarfin wuƙa da nama a lamuran jagaoranci da alfarma. Ita kuwa alfarma a Nijeriya ta fi samuwa ga waɗanda ke biyayya ga muradun fadar shugaban ƙasa.

Ƙarfin jam’iyyun adawa ya sa lalle sai an rarrashe su matuƙar APC za ta cimma burin ‘yan takarar ta su haye karaga. Tuni masu son takarar daga na jam’iyya da masu bin ’yan majalisa don samun goyon baya ke yin taruka ko ziyartar ’yan majalisar don neman goyon baya tun da a kan kaɗa ƙuri’a ne a lokacin zaven shugabannin majalisar.

Sabbin ‘yan majalisar wakilan Najeriya sun ce za su haɗa kai don magance zargin da a ke yi wa majalisa na zama ‘yar amshin shatan sashen zartarwa. A baya-bayan nan a APC an fi kalawa ko ɗaukar majalisa ta 9 da ke kammala aiki da cewa ta fi zama ’yar amshin shata ta yadda duk abun da ya fito daga fadar shugaban ƙasa ba ya samun cikas wajen amincewa.

Wannan ya biyo bayan yadda shugaba Buhari da jam’iyyarsa ta APC su ka mara baya ga Ahmed Lawan da Femi Gbajabiamila su ka zama shugaban Majalisar Dattawa da wakilai a shekara ta 2019. Majalisar da ta gabaceta ta 8 ta yi ta zaman doya da manja da fadar shugaba Buhari inda har ta kai ga tsohon shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya yi ta fama da ƙalubalen shari’ar aikin da ya yi tun gwamnan Kwara da hakan ya kai ga har isa Kotun Ƙoli.

Shi ma Kakakin Majalisar Wakilai na lokacin Yakubu Dogara bai kwashe niƙar da waƙa ba don duk asalin hawan su muƙaman ba da mara bayan sashen zartarwa da jam’iyya ba ne.

‘Yan majalisar dai da ke taruka daban-daban a Abuja; sun ce za su mara baya ga kakaki da sauran shugabannin majalisa ne da za su kare muradun dimokraɗiyya maimakon na ƙashin kai.

Sabbin ‘yan majalisar daga dukkan jam’iyyu su 243 cikin adadin ‘yan majalisa 360 wanda hakan ya nuna har dai za su yi aiki tare to za su iya kawo sauyin da su ke hanƙoron yi cikin sauqi. Aƙalla a yanzu an samu biyu daga cikin ’yan majalisar da Allah ya yi wa rasuwa gabanin rantsuwar shiga ofis.