Jarumin Nollywood, Saint Obi ya riga mu gidan gaskiya

Fitaccen jarumi a masana’antar shirya fina-finai ta Nollywood, Saint Obi, ya bar duniya yana da shekara 57.

Jarumin ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya.

Bayanai sun ce jarumin ya cika ne a ranar Lahadin da ta gabata, 7 ga Mayu, a gidan wata ‘yar uwarsa.

A cewar rahotanni, rashin jituwa a tsakanin ‘yan uwansa ya haifar da tsaiko wajen sanar da rasuwar marigayin a hukumance.

Majiya ta ce bayan rasuwar marigayin a ranar Lahadin, an ɗauke gawarsa zuwa ɗakin adana gawarwaki na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH).

Jaridar Intel Region ta rawaito cewar, a baya-bayan nan Saint Obi ya koma wajen wata ‘yar uwarsa da zama a Jos, babban birnin jihar Filato, kuma an ga yadda ake ta ɗaukar sa zuwa asibiti.