Shirin AGILE ya yunƙuro don inganta ilimin ‘ya’ya mata a Gombe 

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARO a Gombe

Shirin nan na inganta ilimin ‘ya’ya mata na AGILE a Jihar Gombe, a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar ya bayyana cewa zai mayar da ‘ya’ya mata sama da 10,000 a faɗin jihar. 

Masana a wajen taron da Bankin Duniya ke tallafawa, zai ƙara damar ‘yan mata na samun ilimi a jihar. 

Sun bayyana hakan ne a wani taron yini ɗaya na tattaunawa da wayar da kai ga ƙungiyoyin agaji, CBOs, da ƙungiyoyin farar hula (CSOs) da aka gudanar a Gombe.

Dakta Amina Abdul, shugabar shirin AGILE a jihar Gombe, ta ce shirin zai mayar da hankali kan ƙarfafa ‘yan mata ta hanyar ilimi, musamman ‘yan mata masu shekaru 10 zuwa 20, ta hanyar magance matsalolin da ke hanasu samun ilimi.

Ta bayyana cewa shirin zai yi rijistar ‘yan mata 10,000 a faɗin jihar, domin tabbatar da sun koma makaranta. 

Hakazalika, za a aiwatar da tsare-tsare kamar bayar da tallafin karatu, gyaran makarantu, da kuma shigar da iyaye cikin shirin domin cimma burin inganta ilimi a tsakanin ‘yan mata.

Misis Gloria Usman, Daraktar ƙungiyar ɓoice of Hope, ta yaba wa shirin AGILE, tana mai cewa zai taimaka wajen magance matsalolin da ke hana ‘yan mata samun ilimi. 

Ta yi kira da a tabbatar da aiwatar da shirin yadda ya kamata don cimma burinsa.

Dokta Ishiyaku Adamu, shugaban ƙungiyar JONAPWD na jihar, ya ce shirin zai taimaka wajen magance ƙalubalen da ke hana yaran samun ilimi, musamman yara masu buƙatu na musamman, ta hanyar samar da kayan aiki da horas da malamai masu kula da su.

By ukarofi