Shirin Mayar da Alheri da Alheri: Ƙalubale ga manyan Arewa

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Sanannen abu ne mutanen Arewa ba su cika tuna baya ba, kuma kishinsu ga al’ummarsu na da rauni matuƙa, wannan ne ta sa duk da tasirin Arewa a sha’anin riƙe madafun iko na ƙasa, bai sa Arewa ta  zama gagara tsara a Nijeriya ba, bai kuma hana takwararta zarce ta a ɓagaren cigaba ba, duk da cewa, Arewa ce uwa a sha’anin mulkin Nijeriya.

Duk wani da ke son faɗin gaskiya, ba zai iya cewa Kudu ta fi Arewa hanyoyin wadata ƙasa ba, ba zai iya cewa,  ta fi arziki ba, ba zai iya cewa, Kudu ta fi Arewa fiƙira ko ƙirƙiran ababen da za su iya kai ƙasa gaba ba. Saidai zai iya cewa, Kudu ta fi Arewa kishin kai da kuma waiwayen baya.

Abinda nake ƙoƙarin faɗa a nan shi ne, manyan Arewa na mantawa da silar samun kansu a muhallin da suke kai, wannan ne ke sa ba sa tunanin mayar da alheri da alherin da aka yi masu.

Kafin mai karatu ya kai ga tambayar ma’anar mayar da alherin da aka yi masu zan yi ƙarin bayani, a lokacin da wani ɗan siyasa ya yi aniyyar neman damar riƙe wani daga cikin madafun ikon ƙasar nan, abu mai muhimmanci da yake fatan samu shi ne, yardar mutanen shi. Idan za a tambaye ni waye mutanen shi zan ce ‘yan Arewa. Saidai abin takaicin lokacin da mutanen nasa suka yi tsayin daka, suka yi iya yin su don ganin sun kai shi ga kujerar da yake nema, sai kuma ya rufe idonsa daga ganin su har sai ya sake neman su.

Anan ba ina zance da kalaman siyasa ba, domin ina magana ne kan dukka ɓangarorin, ciki kuwa har da masu mora daga cikin albarkatun da Arewa ke da su, misali; masu haƙar ma’adanu, masu sarrafa wasu ababe da aka azurta Arewa da su, kai har ma manoman da suka kai mataki na ƙololuwa a harkar morar ƙasar da take shimfiɗe a Arewacin Nijeriya wadda Allah Ya albarkaceta fiye da saura ta fuskar noma.

Manyan Arewa kan kasa kaifafa tunaninsu tare da zurfi a tunanin makomar Arewa a lokacin da ta cigaba da tafiya a halin da take ciki. Ko ba komai dai, ko sun so ko sun ƙi, Arewar dai ita ce tushen su, duk nisan jifa, wata rana dai za ta sauka, wato duk inda suka tafi, za su dawo mata.

Masu azancen zance na cewa, “ba a kashi wurin da ake cin abinci” ma’ana dai ga hankali, duk inda arzikinka ke fitowa, to yana da kyau ka ba shi kulawa ta musanmman, wanda idan ma ya gyaru amfanin kanka ne.

Ba sai mun tafi da nisa ba, idan muka ɗauki matsalar tsaro kawai za ta goyi bayan maganganuna ta kowanne ɓangare. Arewa na fama da rashin ilimi, wanda ba sai an kai ga gwamnati ba, mutanen Arewa da Allah Ya tarfawa garinsu nono kawai za su iya bayar da gagaruwar gudunmuwa a ɓangare. Wanda kuma da akwai ilimi to fa da da yawa ba su samu kansu a harkar ta’addanci ba. Za ku aminta da hakan idan kuka yi waiwaye kan wasu tattaunawa da ake yi da wasu masu aikata irin waɗannan aika-aikar.

A wani ɓangare akan samu yunwa a layin farko da ke yaƙi da walwala da kwanciyar hankalin Arewa, kamar yadda Bature ya ce, wai “a hungry man, is an angry man” ma’ana dai duk wanda cikinsa ke ɗauke da yunwa, to fa ba abinda ba zai iya yi don cika shi ba. Wannan ne ya sa harkar ta’addanci ke yaɗuwa kamar wutar daji a tsakanin jama’armu.

Idan mun koma ɓangaren lafiya da sauran ababen more rayuwa da mutane ke buƙata, muna da manyan da za su iya yin wani abiu, ko da aljihunsu ko a faɗa a baki a yi sakamakon kusanci da tasirinsu ga gwamnati, amma me, sai su kawar da ido.

Mai karatu kada in ja ka da nisa har mun fita daga layi, na ɗauki shirin Mayar da Alheri da Alheri, wato Giɓing Back Initiatiɓe na gidauniyar tshohon gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Attahiru ɗalhatu Bafarawa, don ya zama wata hujja da zan kafa da za ta kaini ga manufan kiran da nake yi ga manyan Arewa, don fatan ya zama izna ko tsani da za su iya kwaikwayo don ganin sun tsamo Arewa daga halin da ta ke ciki,kamar dai yadda masu iya magana suka ce, “hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka” kuma “hannu da yawa maganin ƙazamar miya”.

Kafin in aikata ƙudurina, zan so mai karatu ya fara da sanin wannan shiri na Mayar da Alheri da Alheri.

Shi dai wannan shiri, wanda sunansa kawai zai iya ganar da mai karatu alƙiblar da ya dosa, wato wata hanya ce da shi tsohon gwamnan zai mayar da alherin da mutanen Sakkwato suka yi masa da alheri daga wurinsa.

Da wannan ne ya ware biliyan ɗaya, ya ce, a yi wa mutanen jihar da ya yi zama shugaba gare su a tsakanin shekara ta 1999 zuwa ta 2007, alheri don nuna masu godiya, da kuma fatan Allah Ya yafe masa kura-kurai da ya yi yayin da yake matsayin gwamna, don duk ɗan mutum ɗan tara ne bai cika goma ba, kamar yadda ake faɗa.

Waɗannan kuɗaɗen ya miƙa su a hannun  mutumin da ya yi shuhura a ɓangaren sha’anin aikin  jin ƙai da kwatanta adalci, wato Injiniya Muhammad Lawal Maidoki, Sadaukin Sakkwato, kuma shugaban Hukumar Zakka da Waƙafi ta Jihar Sakkwato, inda za mu iya cewa tabbas an kai aiki a inda ake iya yinsa.

Bayan dogon shiri, an zaƙulo ɗaliban da suka kammala sakandare, suke na niyar zuwa mataki na gaba, amma a ɓangarorin aikin lafiya guda goma-goma daga kowacce ƙaramar hukuma da ke faɗin jihar, don ba su damar yin jarrabawa ta gwaji, waɗanda suka ci su samu damar karatu kyauta a ɓangaren lafiya, wato scholarship. Wanda cikin tallafin har da kuɗin shiga motar zuwa makaranta.

Wani abin birgewa ga wannan shirin kuwa, shi ne yadda aka bi cancanta yayin tatancewa ta hanyar yin jarrabawar gwaji ga mutanen da aka kawo, wanda hakan na nuni da rashin san kai a ciki.

Sai kuma aka ware wasu daga kuɗaɗen aka siyo kayan abinci, don rabawa mabuƙata, tsofafi, uwayen marayu da kuma masu lalura ta musamman, don bayar da gudunmuwa a ɓangaren yaƙi da yunwa. Yadda aka kasa abincin kuwa shi ne, kowacce ƙaramar hukuma daga ƙaramar hukuma 23 da ke Jihar Sakkwato, an ware mata buhu 100, don ta rabawa waɗannan bayin Allah da muka ambato, ƙarƙashin jagorancin Uban ƙasa na yankin, manyan limaman yankin, shugaban ƙaramar hukumar yankin da kuma wakilai na babban kwamiti da ƙaramin kwamiti na yankin.

Ba a tsaya a iya nan ba, domin shirin ya yi wa mata zawarawa da uwayen marayu tanadi na dogaro da kai, inda aka ce kowacce ƙaramar hukuma ta bazama a tsakaninta ta zaƙulo bayin Allah zawara, da uwayen marayun da ba su da majingini don koyar da su sana’ar da za su dogara da kansu da taimaka wa ‘ya’yansu, wanda hakan zai hanasu shiga halin baɗala ko ƙasƙanci, ya kuma ba wa yaransu kariya daga shiririta.

Su ma dai masu lalurar ƙwaƙwalwa an taɓo su, domin kowacce ƙaramar hukuma za ta bayar da mahaukata biyu da za a kaisu asibiti tare da kula da su har zuwa lokacin da hukuncin Allah zai tabbata akansu na waraka.

Masu azancin magana sun ce, “ana batun duniya akan yi na ƙiyama” su ma dai mamatan wannan shirin bai manta da su ba, domin inda suka tafi muma muna kan hanyar zuwa. An buƙaci ƙaramin kwamiti na kowacce ƙaramar hukuma tare da haɗin gwiwa da Uban ƙasa na yankin su binciko maƙabarta biyu da ke buƙatar tallafi, ya Allah na ƙara mata girma ne sakamakon cika, ko bangonta ya faɗi, gyaran hanyar isa gare ta da sauransu don ganin su ma tallafin ya kai gare su.

Sai kuma masu lalura ta musamman da suke cikin halin ha’ula’I guda biyu daga kowacce ƙaramar hukuma don kula da su har zuwa inda Allah ya ƙaddara.

Akwai shiri na musamman ga masu matsalar muhalli, za a zaƙulo bayin Allah da gidajensu ke da matsala ta gyara, amma ba mai yawa ba, kamar dai faɗuwar katanga, rufi da ire-irensu don taimaka masu suturce muhallinsu.

Sai sha’anin ruwa da za a yi rijiyoyi biyu ga kowacce ƙaramar hukuma da kuma gyara mata bohal biyu da suka lalace a yankin nasu.

Mai karatu idan ka bi wannan tsari da karatu na fahimta, tabbas za ka kwaɗaitu da cewa, ina ma wannan lamarin ya zama abin kwaikwayo ga sauran manyan Arewa.

Ya makomar Arewa za ta kasance yayin da kowanne ɗan siyasa ko mai moriyar Arewa zai yi koyi da irin wannan shirin na Giɓing Back Initiatiɓe?

Aisha Asas

Editar Adabi da Mata a jaridar Blueprint Manhaja.

By ukarofi