


Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi alƙawarin yin amfani da ƙarfin ikon da kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba shi wajen tabbatar da cewa sojojin Najeriya sun samu wadatattun kayan aiki domin tunkarar ƙalubalen tsaron da ƙasar ke fuskanta.
Shugaban ya furta hakan ne ta bakin Mataimakinsa Kashim Shettima wanda ya wakilce shi a wajen bikin yaye manyan hafsoshin soji ƴan ajin 32 da suka samu ƙarin horo kwalejin tsaron kasa a Abuja.
Sanata Kashim Shettima ya ƙara da cewa, shugaban ya amince da mahimmancin samar da kyakkyawan jagoranci a matsayin ginshiƙin makamin magance matsalolin tsaro da samar da cigaban Najeriya.
Shugaban ya kuma yaba wa ɗaliban da aka yaye bisa gudunmawar da suke bayarwa, musamman a ɓangaren bincike da bayanan da suka samar kan yadda za a yi amfani da harkar haƙo ma’adinai wajen samar da tsaro da cigaban ƙasa Najeriya.
