Kotun Ƙoli ta tabbatar da Ododo na APC a matsayin gwamnan Kogi

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Kotun ƙoli ta tabbatar da Usman Ododo na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kogi da aka yi a ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023.

Hakan na zuwa ne bayan da kotun ta yi watsi da ƙarar da abokin karawar sa na jam’iyyar SDP, Murtala Ajakaya shigar wanda ya ƙalubalanci sakamakon zaɓen.

A yayin hukuncin, kotun ƙoli ta ɗora daga kan hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yi a ranar 27 ga watan Mayu, 2024 kan batun inda a nan ma Ododo ne ya yi nasara.

Tawagar masu hukunci na mutum biyar ta ce zargin rashin kiyaye dokar zaɓe daga ɓangaren Ododo bai samu kariya ba daga ɗan takarar na SDP.

Sannan, batun ƙaryar shekaru da kuma shaidar bogi, a kan gabatar da su ne gabannin zaɓe wanda babbar kotun tarayya ce ke da alhakin ji da irin yanayin.

Hukumar zaɓe ta ƙasa, INEC ta ce Ododo ya yi nasara ne da ƙuri’u 446,237 inda ya doke Mista Ajaka wanda ya zo na biyu da ƙuri’u 259,052.

By Babaji