Shugaban ƙaramar Hukumar Bursari ya nemi goyon bayan ‘yan adawa a Yobe

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sabon Zaɓaɓɓen Shugaban ƙaramar Hukumar Bursari a jihar Yobe, Hon. Lawan Bukar Guba, ya yi kira ga ‘yan takarar jam’iyyun adawa da suka gudanar da zaɓen da shi da su ba shi haɗin kai don ciyar da ƙaramar hukumar gaba.

Ku tuna cewa Guba yana ɗaya daga cikin shugabannin ƙananan hukumomin jam’iyyar APC 17 da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar ta ayyana a matsayin waɗanda suka lashe zaben ƙananan hukumomin da aka gudanar a jihar Yobe ranar Asabar.

A wani kira na haɗin kai, Guba ya gayyaci ‘yan takarar jam’iyyar adawa da su haɗa kai don ci gaban yankin Bursari da jihar Yobe baki ɗaya, yana mai cewa: “Dole ne mu haɗa qarfi da ƙarfe domin cimma manufa ɗaya ta raya ƙaramar hukumar Bursari da jihar Yobe”.

Guba a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, kwafin da aka aike wa Blueprint, ya bayyana godiyarsa ga gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, bisa takararsa a ƙarƙashin tutar jam’iyyar APC, ya kuma yi alƙawarin tabbatar da ingancin shugabancinsa.

Shugaban majalisar da aka zaɓa ya kuma jaddada kiran da gwamnan ke yi a kullum na ƙarfafa matasa da tallafa wa marasa galihu, inda ya yi alƙawarin ci gaba da gudanar da ayyukan.Ya ce: “Insha Allahu irin jagoranci mai hangen nesa na mai girma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, za a ci gaba da yi, kiraye-kirayen da mai girma gwamna ya yi ga mu zaɓaɓɓun wakilai a kowane mataki, a matsayinmu na Shugaban Bursari na ƙarfafawa matasa da masu ƙaramin ƙarfi gwiwa.”

Guba ya kuma yaba da irin gagarumin goyon bayan da ya samu daga ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Bursari a majalisar dokokin jihar, a lokacin zaben da kuma bayan zaben.Ya kuma miƙa godiyarsa ga shugaban jam’iyyar na jiha Honorabul Muhammad Gadaka da ɗaukacin ‘ya’yan jam’iyyar na Unguwa bisa goyon bayan da suka ba shi.Guba ya yaba wa hukumar zaɓe ta jihar bisa yadda ta gudanar da zaɓen kansiloli, ya kuma godewa shugabannin al’umma bisa goyon bayan da suke ba shi a kodayaushe, inda ya yi alƙawarin samar da ribar dimokradiyya da ta dace da manufar Gwamna Buni.

By ukarofi