Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Alƙaluma na nuni da cewa daga cikin ma’aikata miliyan 76 da ke Nijeriya, miliyan 5.3 ne za su amfana da ƙarin albashin da ake shirin yi.Hakan na zuwa ne duk da cewa bincike ya gano cewa Nijeriya na daga cikin masu biyan albashi mafi muni a Afirka.Wannan kuma na nufin duk abin da ma’aikatan da za a yi wa ƙarin suka samu, za su raba su kai tsaye ne ko a fakaice tare da sauran ’yan ƙasar sama da da miliyan 224.
Alƙaluman Hukumar Ƙididdiga ta Kasa (NBS) sun nuna cewa ’yan Nijeriya miliyan 1.5 ne ke aiki da gwamnatin tarayya.Wasu miliyan biyu na aiki da gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi, miliyan 1.8 kuma a kamfanoni masu zaman kansu.
A yayin da ake ci gaba da kai ruwa rana kan ƙarin mafi ƙarancin albashi a Nijeriya, Farfesa Kemi Okuwa ta Cibiyar Nazarin Zamantakewa da Tattalin Arziki ta Nijeriya (NISER), ya bayyana cewa ƙasar ce ta 44 a Afirka wajen biyan mafi ƙarancin albashi.
Har yanzu dai ana kai ruwa rana tsakanin ƙungiyar kwadago da gwamnatin ƙasar kan sabon mafi ƙarancin albashi.Hasali ma, ana ja-in-ja tsakanin matakan gwamnatin ƙasar uku, domin kuwa jihohi da ƙananan hukumomi na cewa ba za su iya biyan sabon albashin N62,000 da gwamnatin tarayya take so ba.
Ƙungiyoyin ƙwadagon Nijeriya dai sun daɓe da yin watsi da ƙarin mafi ƙarancin albashin zuwa N62,000 da gwamnatin tarayya ta yi.Duk kuwa da cewa ƙungiyar gwamnonin Nijeriya (NGF) da ƙungiyar ƙananan hukumomin Nijeriya (ALGON) sun ce ba za su iya biyan wannan adadi ba.
Wani abin ban mamaki, ƙungiyar ƙwadagon ta ce ba za ta amince da duk abin da ya gaza N250,000 a matsayin mafi ƙarin albashin da ma’aikata ba.
Masana da dama da masu tsokaci, ciki har da wasu ’yan majalisar dokokin kasar na ganin kara mafi karancin albashin zuwa N100,000 zai daukaka rayuwar ma’aikata ba tare da haifar da karin hauhawar farashin kayayyaki da zai kara yin illa ga tattalin arzikin kasar ba.
Ma’aikata miliyan 5.3 ne za su amfana
Nijeriya mai yawan al’umma miliyan 229, na da yawan ma’aikata miliyan 76, amma ba dukkan ma’aikatan ne kai tsaye za su samu ƙarin albashi ba saboda wasu dalilai, in ji manazarta.
A yayin da masana ke ganin cewa ma’aikatan gwamnati sun fi cancantar karin fuskar albashi, amma sun lura cewa idan gwamnati na son magance matsalar albashin da ake fama da shi a kasar nan, dole ne duk matakan gwamnati su kara kaimi wajen rage tsadar rayuwa.
Dole ne kuma su samar da yanayin da za su iya bunkasa harkokin kasuwanci, wanda hakan zai inganta rayuwar miliyoyin ’yan kasa da ke cikin fatara.
Masana dai na ganin cewa da yawa daga cikin ma’aikatan gwamnati na karbar bashi ko kuma amfani da wasu hanyoyin haram wajen samun karin kudaden shiga domin su iya biyan bukatun rayuwa na abinci, matsuguni, lafiya, ilimi da sufuri da dai sauransu.
Mafi ƙarancin albashin ma’aikatan gwamnatin tarayya, wanda a halin yanzu yake N30,000, an kara shi ne a shekarar 2019, lokacin da hauhawar farashin kayayyaki ya kasance tsakanin kashi 11 zuwa 12%.
Sai dai kuma yanzu darajar Naira ta ragu da kashi 276% cikin ɓari idan aka kwatanta da yadda take a 2019.
Hakan na daga cikin dalilan neman inganta tsarin albashi.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za biya mafi karancin albashin da ba zai gagare ta ba.
A jawabinsa Shugaban ƙasar a lokacin bikin Ranar Dimokuraɓiyya ya sanar da Majalisar Dokoki ta kasa cewa nan ba da jimawa ba zai aike mata takardar dokar sabon mafi ƙarancin albashi na kasa.
Daga bisani ya ta yi wani jawabin a daren Larabar a dakin taro na gidan gwamnati dake Abuja, a lokacin liyafar bikin cika shekaru 25 na ranar dimokuradiyya.
Da yake magana kan batun mafi karancin albashi ga shugabannin majalisar dokokin kasar, wanda shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya wakilta, shugaba Tinubu ya ce gwamnati za ta yi abin da ya kamata, amma abin da za ta iya za ta biya.
“Shugaban Majalisar Dattawa, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, za ku sami sanarwa kan mafi karancin albashi. Za mu yi abin da Najeriya za ta iya, abin da za mu iya, ba abin da ake so ba, za mu yi daidai ruwa daidai kurji,” inji Shugaban.
