Gwamnatin Kano ta sake yin rusau, ’yan kasuwa sun koka

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

’Yan kasuwa dake harkokin kasuwanci a zagayen gefen filin Idi sun koka bisa yadda gwamnatin Jihar Kano ta sa aka rushe musu shagunansu na kwantenoni duk kuwa da irin gudunmawa da suka ce sun bayar domin tabbatar da nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf.

A safiyar ranar Laraba ne dai jami’an hukumar tsara birane suka dirarwa shagunan kwantainoni da rushe su da hakan ya so jawo hatsaniya sakamakon jifa da wasu daga yan kasuwar suka soma yiwa jami’ai  masu baiwa aikin rusau din kariya kafin daga baya jami’an  yansanda suka kawo ɓauki.

’Yan kasuwar sun bayyana  cewa ba a basu wata   mafita ba ko wani dogon wa’adi da za su kwashe kayayyakin su, dan wa’adi da aka basu ma bai ida cika ba sai kawai aka zo ana rushe musu kayyaki da hakan ya jawo musu dinbin  asara.

Sai dai a bangaren hukumar raya birane ta Jihar Kano.An jiyo shugabanta  Ibrahim Yakub Adamu ya ce sai da aka baiwa yan kasuwar wa’adi kafin ayi aikin rusa kwantenonin kuma anyi haka ne  domin inganta tsaro Sakamakon yanda ake fakewa da Kasuwanci ake aikata laifuka da suka hada da  sayar da miyagun kwayoyi da kwacen waya, sakamakon haka kwanakin baya   an tsinci gawar wata budurwa da aka kashe a wurin. Sai dai wasu daga ’yan kasuwar sun yi kira ga Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kawo musu dauki, domin sun shiga wani mawuyacin hali sakamakon rushe musu kwantenoni da tebura da hanasu sana’a a wajen ba a kuma sama musu wani wajen ba

By ukarofi