Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI a Abuja
Tsohon shugaban Ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan ya yaba ma Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki kan amincewa da biyan Naira 70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan jiharsa.
Ya fadi haka ne a ranar Laraba yayin hira da manema labarai a lokacin ƙaddamar da bude sabon sakatariyar ma’aikata a Benin, babban birnin Jihar.
Johnathan ya ce, wannan wani mataki ne da zai inganta walwala da jin daɗin al’ummar Jihar da kuma gwamnatinsa.
Goodluck ya ƙara da cewa kasancewarsa jajirce kuma mai hangen nesa ne suka sa ya yi wannan babban abun a yaba duk da ƙalubalen tattalin arziƙi a Najeriya wanda hakan abun koyi ne ga takwarorinsa
