Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ofishin Shugaban Ma’aikata na Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ya dakatar da Babban Sakatare a Ma’aikatar Harkokin Ƙasashen Waje, Ambasada Ibrahim Lamuwa, bisa zargin cin zarafin mata.
Shugabar Ma’aikata, Folashade Yemi-Esan, ta ce za a dakatar da sakatare na dindindin har sai an kammala bincike cikin gaggawa kan zargin da ake masa.
Wani babban darakta a OHCSF ya shaida wa wakilinmu a Abuja cewa, “an dakatar da sakatare na dindindin har sai kwamitin da a ka kafa ya kammala bincikensa.”
An tattaro cewa, biyo bayan koken da Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya gabatar a kan Lamuwa, Hukumar HoS ta kafa wani kwamiti da zai binciki lamarin.Wanda ya shigar da ƙarar da Tuggar ya gabatar ita ce Simisola Ajayi, wacce ta zargi Lamuwa da cin zarafin mata.
Ajayi, a cikin ƙarar da lauyanta Femi Falana (SAN) ya shigar, ta bayyana zargin cin zarafi.
A cikin wata wasiƙa da ya aike wa Shugaban Ma’aikata a ranar 27 ga Mayu, 2024, Tuggar ya bayyana damuwarsa kan yadda zarge-zargen da ke tattare da sakatare na dindindin.
“An tilasta ni in rubuta domin in sanar da ku ƙarar da aka shigar a kan babban sakataren ma’aikatar harkokin wajen ƙasar, Ambasada Ibrahim Adamu Lamuwa kan zargin cin zarafi.
“Da yake la’akari da girman al’amarin, ina ganin ya dace in jawo hankalinku zuwa gare shi kuma ku bi shi yadda ya kamata,” inji ministan a cikin wasiƙar.
Wani jami’in da ke da masaniya kan lamarin ya shaida wa wakilinmu a ranar Laraba cewa, bayan samun wasiƙar Tuggar a kan zargin da ake yi wa Lamuwa, Hukumar HoS ta kafa kwamitin bincike.
Jami’in wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda yadda lamarin ya kasance, ya ce, “Eh, shugaban ma’aikatan ya kafa wani kwamiti da zai binciki lamarin baki ɗaya. Akwai hujjoji, waɗanda za a gabatar da shaidu waɗanda su ma za a gayyaci su yi magana a kan lamarin, don haka ba batun da za a birne ba ne.
“Ministan (Tuggar) shi ma yana matuƙar buƙatar sakamakon. Ma’aikatar Harkokin Waje ma’aikata ce ta musamman da ke aiki ko da a wajen ƙasar, don haka ba za ka yi tsammanin za a birne wani batu na irin wannan ba.”
Ajayi ta kasance, a cikin ƙarar mai kwanan wata 29 ga Mayu, 2024 kuma aka aika zuwa Tuggar, ya zargi sakatare na dindindin da cin zarafin mata.
Takardar ƙarar mai ɗauke da sa hannun Adebayo A. Oniyelu LP na Falana & Falana’s, mai taken “Request For An Investigation Of Amb. Ibrahim Lamuwa na Cin Zarafi da Wariya a hukumance.”
