Shugaban AMAC, Candido ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan wakilin Jaridar Blueprint a Nyanya

Shugaban Hukumar AMAC ta Abuja, Hon. Abdullahi Adamu Candido, ya ziyarci iyalan marigayi Baba Yusuf, domin jajanta musu bisa rashin da ya same su.

Marigayi Yusuf wanda wakilin Jaridar Blueprint ne a halin rayuwarsa, ya rasu ne ranar Talatar da ta gabata, 4 ga Agusta 2021, a gidansa da ke yankin Nyanya Gwandara a jihar Nasarawa.

Kafin rasuwarsa, marigayi Yusuf mamba ne na tawagar ‘yan jaridar Hukumar AMAC.

Sa’ilin da yake isar da ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, Hon. Candido ya bayyana marigayin a matsayin ɗan jarida mai aiki tukuru daidai da dokokin aikin jarida.

Haka nan, ya nuna damuwarsa kan yadda za a yi ‘ya’yan marigayin su uku su ci gaba da karatu ba tare da fuskantar wani tsaiko ba, wanda hakan ya sa ya ɗauki alƙawarin bai wa matar marigayin aiki domin ta samu hanyar kula da sha’anin karatun yaran.

A nata ɓangaren, matar marigayin ta yi nuna godiyarsu bisa ga ziyarar da kuma karamcin da Hon. Candido ya nuna musu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *