Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Shugaban Kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu, a ranar Alhamis, ya ɗora alhakin aarancin kayan abinci da tsadar kayan masarufi a Nijeriya a kan ayyukan wasu ’yan kasuwa masu son kai.
Wannan dai na zuwa ne a yayin da ’yan kasuwar suka yaba wa Shugaba Bola Tinubu kan yadda ya ɗage haraji kan shigo da abinci a ƙasar nan.
Rabiu ya bayyana haka ne a taron shekara na kamfanin karo na 7 a Abuja.
Ya ce, “Kayan BUA sune mafi arha a kasuwa. Kuma da yake muna da wasu kamfanoni da ke samar da irin waɗannan kayayyaki, yana da wahala a rage farashin su. Misali, a watannin baya, farashin fulawa ya kai Naira 70,000 kan kowace buhu. Mun riƙe namu akan N50,000 na wani ɗan lokaci don ƙoƙarin tilasta wasu kamfanoni su ma su sauƙar da na su. Amma da suka ga abin zai faru, da gangan suka daina samar da fulawa, kuma farashin ya ci gaba da hauhawa.
“Don haka a lokacin da muke sayarwa a kan N50,000, diloli sun ƙara Naira 20,000 inda aka sayar da ita kan N70,000 a kowace buhu. A wani lokaci kwastomomi na oda a akan kusan Naira miliyan 20 na kowace babbar mota mai ɗaukar tan 75 na fulawa. Eh ya faru. A lokacin da muke badawa a kan Naira 50,000, muna ta ƙururuwa da addu’o’in neman saukowar kaya, wasu kamfanoni ba su ji daɗin yadda muka rage farashin ba.
“Hakan ya sa kwatsam suka daina samar da kayayyaki don haifar da ƙarancinsa. Da wannan ƙarancin, farashin ya ci gaba da hauhawa. Don haka wannan ne babbar matsalar. Da muka ga haka, mun san bai dace ba mu ci gaba da sayarwa a kan Naira 50,000 a lokacin da kasuwar ke kan N70,000. Abubuwan da muke samarwa suna da yawa, amma akwai wasu kamfanoni biyu da suka fi mu girma.
Duk da haka, mun yi imanin cewa nan da shekara mai zuwa, za mu fi su girma.”
Wannan ci gaban ya zo ne kwanaki kaɗan bayan kamfanin BUA na abinci ya sanar da cewa, ya ƙulla yarjejeniya da zaya daga cikin manyan kamfanonin samar da taliya a duniya, FAɓA, domin faɗaɗa aikin samar da taliya.
Rabiu ya ce haɗin gwiwa da katafaren kamfanin na ƙasar Italiya ya yi daidai da dabarun da kamfanin ke bi wajen bayar da gudunmawar samar da abinci a Nijeriya.
A halin da ake ciki, Manajan Daraktan Kamfanin Abinci na BUA, Ayodele Abioye, ya kuma jaddada shirin faɗaɗa kamfanin, wanda ya ce za a yi shi nan ba da jimawa ba.