Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Digital, Farfesa Isa Ali Pantami, ya yi magana a kan irin damuwar da ake ciki game da ƙirƙirarrriyar basira ta AI, inda wasu ke ganin AI na iya raba miliyoyin mutane da ayyukan yi, yana mai cewa fikirar za ta ƙara wa mutane kaifin basira ne.
Pantami ya bayyana ra’ayinsa ne yayin da ya karɓi baƙuncin mahalarta taron PRNigeria na ‘Young Communication Fellowship’ a ofishinsa.
Ya jaddada cewa shirye-shiryen jagoranci da aka mayar da hankali kan haɓaka fasaha na iya haɓaka kwarewar mutane, haɓaka sanin yadda za a riƙa warware matsaloli, da faɗaɗa hanyoyin sadarwar ƙwararru.
“A cikin shekaru masu zuwa, miliyoyin na iya fuskantar asarar aiki yayin da AI ke ɗaukar ayyuka daban-daban,” inji shi.
“Duk da haka, yana da muhimmanci a fahimci cewa ba AI ce kanta ke haifar da asarar aikin gi ba, amma mutane na godaro ne wajen amfani da fasahar. AI ƙirƙirarriyar basira ce irin ta ɗan adam ne; ba ya aiki a karan kansa.”
Yayin da ake tunawa da tsoron fasaha sau da yawa ana bayyana shi a matsayin kawar da Technophobia, Pantami ya bayyana cewa ɗaya daga cikin ma’anar juyin juya halin masana’antu na huɗu shi ne cewa gwaninta a fasaha ba ya buƙatar ilimin kimiyyar kwamfuta.
“Hakazalika, ba kwa buƙatar digiri a Mass Communication don zama ɗan jarida mai samun lambar yabo ko ƙwararriyar hulɗa da jama’a. Wannan juyin juya halin ya ta’allaka ne kan ci gaban mutum da ci gaba da koyo.”
Pantami ya jaddada cewa jagoranci na iya canja rayuwa, ko da ta hanyar ɗan gajeren hulɗa, kuma ya ƙarfafa matasa su nemi jagora daga dattawansu.