Kellyrae ne ya lashe gasar “Big Brother Naija Season 9”, a wannan karon.
Gasar ta rage da ‘yan wasa takwas, inda Kellyrae da Waani suka zama ‘yan wasan ƙarshe.
Wanda aka fara sallama shi ne Sooj, sai Anita, Ozzy, Nelly, Victoria da kuma Onyeka kamar yadda mai gabarta da shirin Ebuka ya sanar.
A ƙarshe, Kellyrae ya zama wanda ya yi nasara a yaƙin neman kyautar Naira miliyan 100, ya zama mai aure na farko da ya samu nasarar gasar.