
Daga BELLO A. BABAJI
An kwantar da Sarki Salman Bin Abdul’aziz As-Saud a asibiti don duba lafiyarsa game da cutar ƙoda.
Kotun Masarautar Saudiyya ta tabbatar da batun cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi inda ta ce, an yi hakan ne la’akari da shawarwari da asibitocin Masarautar ƙasar suka bayar.
A watan Mayu na shekarar nan ne Sarkin, mai shekaru 88 kuma ɗan kasuwa daga gabas ta tsakiya mafi fitar da mai ga ƙasashen duniya, aka duba lafiyarsa a ɓangaren ciwon ƙoda.
Sarki Salman ya bada dokar ta bada damar gudanar da jagoranci daga magajin mahaifin Sarkin wanda yafi tsufa a tawagar manyan ma’aikatan masarautar.
