Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Ibrahim Ishaka, ƙwararre a fannin abinci mai gina jiki a ƙungiyar Abinci da Noma, FAO, na Majalisar Dinkin Duniya, ya bayyana cewa Nijeriya na asarar kusan kashi 50 na kayayyakin amfanin gona.
Ishaka ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya, a wajen wani horo da FAO ta shirya a Yola ranar Asabar.
Ya bayyana cewa asarar amfani gona bayan girbi ya haifar da gagarumin ƙalubale ga fannin noma a Nijeriya, wanda ke yin tasiri ga samar da abinci, ci gaban tattalin arziki, da ɗorewar muhalli.
“Wasu daga cikin waɗannan ƙalubalen sun haɗa da shingen fasaha, rashin ingantattun dabarun girbi, fama da ƙwari, da rashin samun kayan aikin noma na zamani, waɗanda dukkansu ke haifar da asara a lokacin girbi, da ɗabi’un masu amfani da su ke tasiri sosai,” inji shi.
Ishaka ya ƙara bayyana ƙarin abubuwan da ke haifar da asarar bayan girbi, waɗanda suka haɗa da: rashin isassun wuraren ajiya, rashin kulawa da rashin ababen sufuri.
“Waɗannan abubuwan suna haifar da asara mai yawa, musamman ga kayayyaki masu lalacewa kamar ‘ya’yan itatuwa da kayan marmari.
