Shugaban hukumar NTA na ƙasa ya yaba wa Gwamna Nasir

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Shugaban hukumar NTA na ƙasa Salihu Abdulhamid Dembos ya yaba wa Gwamna Nasir bisa ga irin cigaban da ya samar a jihar Kebbi cikin gajeren lokaci.

Ya yi wannan bayanin ne yayin wata ziyara da mashawartan gwamnan kan harkokin kafafen yaɗa labarai suka kai masa a ofishin sa da ke birnin tarayya ƙarƙashin jagorancin kwamishinan yaɗa labarai Alhaji Ahmed Yakubu Birnin Kebbi ranar Talatar nan.
Ya ce akwai buƙatar a haɗa hannu da gwamnatin jihar Kebbi da kuma hukumar gidan talabijin ta ƙasa don bayyana wa duniya irin ayukan cigaba da gwamna Malam Nasir Idris ke yi, kasancewar hukumar ita ce wacce ta ke da rassa ko ina faɗin ƙasar nan kuma da ta ke da ƙwararrun ma’aikata.

Ya bayyana cewa haɗin gwiwar zai inganta yaɗa manufofin gwamnatin da kuma yaƙi da ɓatagarin ƴan jarida da rashin ƙwarewa ke sanya su wallafa labarai da ba sahihai ba da kuma labarai na ƙanzon kurege da ke da hatsarin gaske musamman kan abinda ya shafi zaman lafiya.
Da ya ke jawabi, kwamishinan yaɗa labarai Alhaji Ahmed Yakubu Birnin Kebbi, ya nuna gamsuwar sa bisa ga yadda jami’an hukumar gidan talabijin ta ƙasa ke gudanar da ayukan su a jihar musamman waɗanda suka shafi yaɗa ayyukan cigaba da gwamna Malam Nasir Idris ya samar.

By ukarofi

Leave a Reply