Shugaban PDP na Ƙasa ya naɗa Yusuf Dingyaɗi babban mai taimaka masa kan yaɗa labarai

Daga AMINU AMANAWA a Abuja

Shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa Iyochia Ayu ya naɗa Alhaji Yusuf Dingyaɗi a matsayin babban mai taimaka masa kan harkokin yada labarai da sadarwa.

Naɗin Dingyaɗin dai na ƙunshe ne cikin wata wasiƙa mai kwanan watan  26, ga watan Yuli 2022, kuma take da rattabawar hannun babban sakataren jam’iyyar na ƙasa, Senator Samuel N Anyanwu da bayanin ya ce tuni da naɗin nya soma aiki tun 1 ga watan Yulin shekarar nan.

Dingyaɗi, wanda ƙwararren dan jarida ne kafin naɗin nasa ya yi aiki da kafofin yaɗa labarai daban daban kafin tsunduma harkokin siyasa.

Inda yayi aiki da kafar yaɗa labaran BBC Hausa, da kuma jaridar Nasiha da ake wallafawa a Kaduna da dai sauransu.

Yusuf Dingyaɗi ya kasance mai taimaka wa Marigayi Abubakar Koko (Sarkin Yaƙin Gwandu) a kan kafofin yaɗa labarai, dama tsohon gwamnan jihar Sokoto Attahiru Bafarawa da ma gwamna maici, Aminu Waziri Tambuwal.

Bayan tsunduma harkokin siyasa Yusuf Dingyaɗi ya yi zama kakakin jam’iyyar PDP a jihar Sokoto, sakataren riƙon ƙwaryar jam’iyyar PDP a jihar Kebbi da dai sauransu.