Ina da burin ganin ana bada ilimi kyauta a Nijeriya – Ɗanburam

Daga IBRAHIM A MUHAMMAD

Ɗan takarar Majalisar Dattawa ta Kano ta Tsakiya a inuwar jam’iyyar PDP, Dakta Abubakar Nuhu Ɗanburan, ya bayyana cewa, ƙudurinsa shine, samar da abubuwan cigaba a Kano ta Tsakiya, domin duk abinda ya dami Jahar Kano ya tattara ne a Kano ta Tsakiya.

Ya yi nuni da cewa, a Kano ta Tsakiya ne ake da mafi yawancin ‘yan kasuwa da malamai da kusan dukka abubuwan da mutane ke buƙata suke so su yi na rayuwa. Don haka su yi abinda ya dace a wannan lokaci don tura wakilci da ya dace.

Ya ce, ɗan Majalisar Dattawa na yanzu na yankin, wanda tsohon gwamna ne, me ya yi akan ilimi da nema wa mutane abin yi? Don haka mutumin da ya yi gwamna kullum tunaninsa shine, ya riga ya gama aikinsa, zai yi wahala kaga ya iya ɗaga hannu a majalisa ya kawo wani abu da ya dami al’ummarsa ko ya je wani ofis, ya nemo haƙƙin al’ummarsa, wanda shi a baya ya yi yana ɗan Majalisar Tarayya kuma a gaba ma in Allah Ya ba shi dama, ya zama sanata.

Abubakar Nuhu Ɗanburan ya ƙara da cewa, yana da burin ya ga an tabbatar da dokar ilimi kyauta a Nijeriya, tun daga firamare har sakandire, ya kamata a ce al’ummar ƙasa suna samun ilimi kyauta.

Da kuma yin tsare-tsare na mutane su samu aikin yi in ɗalibi ya gama makaranta ba abin yi. Wanda hakan ke jawo irin abubuwana da ke faruwa na rashin zaman lafiya. Saboda mutane da yawa ba abin yi. Mutum kuma don ya rayu zai iya shiga hanya marar kyau domin ya samu abin taimakon kansa. Wannan shi ne ba a so. Ya kamata a fito da tsare-tsare da dokoki da za su ba mutane na Kano dama, saboda in Kano ta saitu, Arewa ta saitu.

Ya ce, Kano ta Tsakiya na da tasirin da duk wanda zai kasuwanci daga ciki da maƙotan ƙasashe nan yake zuwa, domin gabatar da harkar kasuwanci, wannan shine abubuwan da ya kamata a tsaya akai. Kuma shi babban burinsa ya tsaya ya kare martabar addini wanda ya yi hakan a baya, a gaba ma in dama ta zo zai ci gaba da yin.

Ya ce, a baya a Majalisar Tarayya akwai abubuwa kusan uku da ya tsaya a kansu da suka haɗa da maganar auren jinsi, wanda ya tashi ya ce, bai yarda da maganar ba don addini ya hana. Da aka zo ƙuri’a aka kada ƙudurin. Saboda ba za a ƙaƙaba musu abinda in suka je gaban Allah ba su da abinda za su faɗa ba.

Ɗanburan ya ce, ya kai ƙuduri da kansa na maganar mahajjata da aka karɓi kuɗinsu aka ce wai za a yi musu wani awarwaro da za a gane wanda ya vata a aikin hajji, amma aka cinye kuɗin ba a yi ba, ya tsaya sai da aka dawo musu da kuɗaɗensu.

Sai maganar hijabi da aka hana wata yarinya da ta gama karatun lauya aka hanata sakamako saboda ta sa hijabi, ya ce, bai yarda ba, dole sai an bata, kuma kowa ma a ba shi dama ta addini, saboda hijabi martaba ce da mutunci, don haka duk wani abu na kare martaba da addini za su ci gaba da yi.

Dakta Abubakar Nuhu Ɗanburan ya yi kira ga al’umma akan lokacin zaɓe, su fito su zaɓi cancanta, su zaɓi mutane da zasu tsaya su yi musu aiki, waɗanda zasu gan su su gabatar musu da buqatunsu, in an ba su kuɗi, su karva, amma su zaɓi cancanta. Kuma alamu ya nuna PDP ita za ta dawo mulki cikin yardar Allah, don haka suna roƙon Allah in ya ba su dama, Ya ba su ikon yin aiki na taimaka wa cigaban al’umma.

Ɗan takarar sanatan Kano ta Tsakiya a jam’iyyar PDP ya ce, Jam’yyar APC ta gaza a mulkin ƙasar nan, an zaɓe ta don ta kawo cigaba, amma ba ta kawo ba, ta kawo koma baya a kowane fanni.

Domin da suka zo suna ta ihu kan Boko Haram, Gwamnatin PDP ta kasa komai akai, yanzu sun shigo abin ya fi ƙarfin Boko Haram harkar tsaro ya ta’azzara, ya shiga wani hali da kowanne sashi na cikin damuwa a ƙasar nan, kullum aka tashi sai an ji sabon abu, an farwa nan, an shiga wannan gari, an kashe, an kora mutane, abin ba ƙaramin vaci ya yi ba. Maimakon su zo su gyara abinda suka ce an gagara, sai daɗa lalacewa ya yi.

Ya ce, nan gaba gwamnatin da za ta zo ta PDP sai ta yi aiki tuƙuru don tabbtar da zaman lafiya a ƙasar nan, kuma dama Atiku mutum ne da ya yi mataimakin shugaban ƙasa, ya riga ya san makamar mulki, zai ɗauki matakai don kawo gyara.

Ɗanburan ya ce, ya ji daɗi a wata hira da aka yi da Atiku ya ce, cikin kwanaki 100 na farko maganar tsaro ita ce za ta zama a gabansa, zai tabbatar da cewa, Najeriya an samu saiti na tsaro.