Dandalin shawara

Daga AISHA ASAS

TAMBAYA: Assalamu alaikum. Anty Asas don Allah ki taimaka min da shawara. Wallahi Ina cikin tashin hankali da kuma rashin madafa. Anty ƙanwata ce ta yi cikin shege. Hankalinmu ya tashi sosai har mu ka rasa inda za mu yi da lamarin. Sai dai cikin kwanakin da wannan lamari ya faru, sai na lura, mijina da mahaifiyata na yawan keɓewa. Idan suna magana kuwa da na shigo wurin da suke sai su yi shiru. Abin tun ba ya damuna har ya zo ya fara.

Ana cikin haka kuma sai mahaifiyar tamu ta zo ta daina maganar cikin ƙanwar tawa. Idan na ɗauko zancen a bincike ta a ji wanda ya yi mata cikin sai Mama ta dinga yi min faɗa, wai na cika naci, tunda dai an ce a jira hankali ya kwanta, kuma fa a can baya ta fi kowa buɗa wuta kan sha’anin. To shine fa kaina ya ruɗe, na rasa gane inda ta sa gaba, don har barazana ta ke min wai idan na ci gaba da naci kan batun za mu sami matsala ni da ita.

To nan dai sheɗan ya dinga kitsa min abinda suke tattaunawa da mijina idan ta zo gidan, saboda kusan kullum zuwa take yi. To a kwanakin nan da ta zo sai bayan na bar wurin da take zaune da shi sai na laɓe. A nan na ji ashe mijina ne ya yi wa ƙanwar tawa ciki, kuma Mama ta sani, suna bin hanyoyin da za a zubar da shi ba tare da na sani ba. Don shine kusan ɗauke da iyayena, saboda yana da kuɗi bata so auren ya mutu su rasa abinda yake masu.

To da na dinga kuka ne, na shiga ciki, Ina faɗa da maganganu na ɓacin rai. Shine da na ce sai ya sake ni ne Mama ta yi rantsuwa, wai idan na sa mijina ya sake ni sai ta tsine min. Ki taimaka min Anty Asas yadda kika saba ba mu shawara mai taimakon mu. Wallahi yanzu haka Ina gidan, amma zuciyarta kamar ta fashe, kuma bana son ko jin sunan mijina. Allah Ya biya ki da aljanna.

AMSA: Da farko dai zan fara da cewa, ki yawaita faɗin innalillahi wa Inna ilaihi raji’un, don samun sassauci daga ƙuncin da kike ji, wanda idan bai ragu ba zai iya zama silar kamuwa da cutar da zata iya illata gangar jiki ko zuciya.

Sannan malamai sun sanar cewa, Suratul Yusuf na kawar da baƙin ciki, don haka Ina mai janyo hankalinki kan lizimtar ta. Ko ki karanta da kanki, idan hakan ba zai samu ba ta sanadiyyar tashin iyawa, sai a kunna sautin surar.

Abu na biyu shine, ki dinga tuna wa kanki makomar wanda ya tarbi jarrabawar duniya da haƙuri, makomar wanda ya ci jarrabawar da Allah Ya aiko masa. Ki tuna cewa, Allah na jarabtar bayinSa da ya fi so da mafi girma a jarrabawa.

Sai zancen neman shawara da kike yi. Abu na farko da ya kamata ki fara sani shine makomar aurenku a Musulunci, wanda na ke hasashen kin yi wa kanki wannan tambayar.

To, haramun dai bata taɓa iya kore halas, don haka mummunar alaƙa da ta shiga tsakanin mijinki da ‘yar’uwarki bata lalata aurenku ba, ma’ana Musulunci bai ce dole sai kun rabu ba.

Tabbas abin da mijinki ya yi yana cikin mafi munin abin da zai taɓa yi ma ki, wanda watakila har ƙarshen rayuwarki ba za ki iya yafe masa ba, wanda wannan ne ya kai mu ga gaɓar furucin mahaifiyarki. Idan har za ki iya ci gaba da zama da shi, ki yafe masa, ki daina kallonsa da abin, to za ki samu mafi alkhairin sakamako, saboda biyayya ga mahaifiyarki da kika yi, wanda bayan Allah babu wanda ya kai ta.

Ta sanadiyyar hakan za ki iya samun mafi alkhairi na daga wani mijin ba tare da kin nemi saki ba, sai Allah Ya sa ya sake ki, kuma ya haɗa ki da irin mijin da kowacce mace ke mafarkin samu, albarkacin haƙuri da biyayyar da kika yi.

Sai dai za ki iya haɗuwa da fushin Allah a aikata hakan matuƙar ba ki yi da ƙyar ba. Domin wannan hukuncin ba kowacce mace ce za ta iya aikatawa ba, hakan zai kai mu ga zaɓin da kike da shi na ƙarshe.

Idan har kin san ba za ki iya tausan zuciyarki ba, ba wai na ce a take ba wanda hakan zai yi wuya. Idan kin san ba za ki iya tanƙwarar da ɓacin ranki ba, ba za ki iya yafe wa mijinki ba, ba za ki iya ci gaba da ba shi haƙoƙinsa da ke kanki ba. Idan kinsan za ki yi zaman ɗaukar fansa ne, har wata rana sheɗan ya yi tasiri ki aikata kwatankwacin abinda ya yi, to a nan hukuncin Allah ya shigo, kuma duk inda za ka iya saɓa wa Allah a wani umurni na iyaye, to bai halasta ka yi masu biyayya ba.

Duk da haka ba za ki yi amfani da gautsi ba, ki rarashe ta ta janye furucinta, ko ki yi amfani da wanda ta ke jin nauyi ko ta ke ɗaukar shawararsa. Ba kuma na rana ɗaya ba, ki bada lokaci don ganin ta sauko daga dokin da ta hau. Idan tana gudun yaɗuwar maganar ko ta ƙarar da kike kai nata za ta so ku yi matsaya.

Shawara ta ƙarshe, ita ce, ki yi haƙuri a yanzu da abin yake da zafinsa, kada ki yi yunƙurin ɗaukar mataki har sai kin samu sassaucin tafasar da zuciyarki ke yi. Har sai ƙwaƙwalwarki ta gama ba wa lamarin muhallin da ya dace da shi, hakan zai sa ki yanke hukuncin da zai yi wuya ki yi nadamar yanke shi. Kuma hakan zai iya ɗaukar lokaci, wanda da taimakon addu’a za ki iya yin haka.

A matsayinmu na ‘yan Adam zan iya cewa, ba laifi ba ne bayyana ƙunci ga wanda ya haddasa ma ka shi, asali ma yakan taimaki zuciya wurin saurin waraka daga baƙin cikin. Don haka ƙaurace wa mijinki a yanzu bai zama illa ba, ko bayyana masa yanayin girman ƙuncin da ya sa ki a ciki. Sai dai ki dinga tunatar da zuciyarki darajar aure yayin hakan.

Allah Ya kawo ma ki sauƙin raɗaɗin da kike ji a ranki wanda ba mai iya gane girmansa sai wanda ya ɗanɗana.

Ku aiko da tambayoyinku ta [email protected] ko [email protected]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *