Shugabancin Adamawa: Fintiri ya zarce

Hukumar Zaɓe ta bayyana Gwamna Ahmadu Fintiri na Jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna a Jihar Adamawa.

Sakamakon zaɓe ya nuna Fintiri ya lashe zaɓen cike giɓin da ya gudana a jihar Asabar da ta gabata da ƙuri’u 9,337 wanda hakan ya ba shi damar doke abokiyar hamayyarsa ta Jam’iyyar APC, Sanata Aishatu ‘Binani’ Dahiru wadda ta tsira da ƙuri’u 6,513.

Bayan kammala zaɓen baki ɗaya, alƙaluma sun nuna Fintiri ya tashi da ƙuri’u 430,861, yayin da Binani ta samu ƙuri’u 398,788.

Da yammacin ranar Talata INEC ta kawo ƙarshen tirka-tirkar zaɓen na gwamnan Adamamwa inda ta bayyana Fintiri a matsayin wanda ya yi nasara bayana cika sharuɗɗan da suka dace.