Goman Ƙarshe: Da gaske mata addu’ar neman miji suke yi a tahajjud? (I)

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Fauziyya da Samira (ba sunan su na gaskiya kenan ba) ’yan uwan juna ne, uwa ɗaya uba ɗaya, tazarar da ke tsakanin su ba ta wuce ta shekaru 2 ba, aƙalla za su kai shekaru 30 zuwa 35. Suna zaune ne a wani babban gari dake arewacin Nijeriya. Mahaifin su Alhaji Usman (ba sunan ainihi ba ne) dattijo ne mai rufin asiri daidai gwargwado. Babu abin da ya fi ƙaunar gani a duniya kafin Allah ya ɗauki ransa kamar ya ga auren waɗannan ’ya’ya na sa mata, waɗanda ya bai wa tarbiyya daidai gwargwado, kuma suke da kyan sura irin ta ɗaukar hankali. Amma sai dai kash, har yanzu bai kai ga cimma burinsa ba.

Saboda kuwa ga yaran nasa nan sai shiga da fita suke yi, kamar iyayen mata, amma aure ya gagara. Ba wai sun rasa manema ba ne, amma tsayayyun samari ne suka rasa, ko kuma ba su samu irin mazajen da suke kwaɗayin aure ba, wasu kuma suna zuwa ne ba da niyyar aure kai tsaye ba. Wani lokaci kuma sai ka ga an samu wasu da za su fito su bayyana aniyar su ta a yi aure, amma da zarar an fara daidaita magana sai wasu matsaloli su yi ta giftawa suna kawo cikas a shirin, har ma ta kai ga an fasa maganar, ko da kuwa an ba da sadaki a hannu.

Labarin waɗannan ’yan mata ba qirqira ba ne, da gaske ne, an dai canja sunayen ne domin kawar da kai daga haqiqaninsu. Abin da ke faruwa a rayuwarsu yana faruwa da ɗimbin mata, ƙanana da manya, waɗanda ko auren fari ba su tava yi ba. Matsala ce da ke damun jihohi da daman a arewacin qasar nan, ta yadda har ta kai ga hukumomi da malamai sun zabura don ganin an samu hanyoyin warware waɗannan matsaloli, da ke neman zama annoba a tsakanin al’umma.

Ba baƙon abu ba ne ga masu harka da zaurukan sada zumunta, inda ake ganin wani sabon salon iyayi da ’yan mata suka ɓullo da shi, suna rubuta cewa sun matsu suna son aure, ga hoton su nan ko da mai so ya yi musu magana. Kuma abin mamaki sai ka ga yarinya kyakkyawa tsaleliya son kowa ƙin wanda ya rasa, wai tana tallan kanta. Wannan na nuna irin yadda rashin samun mijin aure yake damun rayuwar ’yan mata da zawarawa a wannan zamani.

Ko da yake akasari wasu na cewa sharrin ’yan soshiyal midiya da masu damfarar mutane, suke sa irin waɗannan hotunan ko sanarwar neman mijin, don su damfari maza masu kwaɗayin fararen mata, ko masu kuɗi da ke son kashewa ’yan mata kuɗi. Hakan ma na iya zama gaskiya, domin lamarin harkar soshiyal midiya ya zama abin tsoro, ba ga mazan ba ba ga matan ba.

Yanzu da aka shiga goman ƙarshe na watan Ramadan, Musulmi a ko’ina a faɗin duniya na ƙara tsananta ibada da neman kusanci ga Allah ta hanyar miqa addu’o’in su cikin sallolin dare na tahajjud da ake yi, don neman dacewa da daren Lailatul Ƙadri, a nasu vangaren ’yan mata na amfani da wannan lokaci ne wajen gabatar da addu’o’in samun mijin aure, da fatan kasancewa a dakunan mazajen auren su kafin wani Ramadan ɗin mai zuwa. Idan mutum ma’abocin shiga zaurukan sada zumunta ne zai yi ta ganin maganganu irin haka, har ma da shaguve ko gugar zana da za ka riƙa gani tsakanin ’yan matan da samari suna tsokanar juna. To, amma wai shin mazan auren ne suka yi ƙarancin ne, ko kuma tsadar rayuwa ce take tsorata su tunkarar auren? Ba za a ce dai babu maza ba, ko babu mata kyawawa, nagari da ake rububin nema a aura ba, a ina matsalar ta ke?

Tambayoyin da suke ta yawo a bakin mutane kenan, me yake jawo wannan jinkiri da ’yan mata ke samu wajen aure, kuma ya za a magance su? Wannan rubutu sakamakon wani bincike ne da na gudanar game da wannan batu da ke ɗaukar hankalin al’umma a yankin mu na Arewa, inda na tuntuɓi ra’ayoyin wasu masana da masu ruwa da tsaki game da yadda suke kallon matsalar a nasu vangaren. Yayin da wasu suka amince da kasantuwar akwai matsalar, wasu kuwa gani suke hakan ba wani abin ɗaga hankali ba ne, domin kuwa canji ne aka samu na rayuwa.

Farfesa Fatima Muhammad Umar, malama ce da ke koyarwa a Jami’ar Bayero da ke Kano ta kuma bayyana cewa dalilai irin su kwaɗayin abin duniya, wayewar zamani ko yaɗuwar ilimi a tsakanin mata da kuma rashin samar da kyakkyawan tsari na wayar da kan matasa game da martabar aure da matsayinsa a rayuwar su, a maimakon tsohon tsarin da ake bi tun zamanin iyaye da kakanni, a matsayin dalilan da ke kawo jinkirin aure a tsakanin matasa a arewacin ƙasar nan. Wannan ra’ayi na Farfesa Fatima ya zo daidai da fahimtar wata fitacciyar marubuciya Malama Rahama Abdulmajid wacce ko da ya ke ba ta yarda mata na jinkirin samun miji ba, tana ganin lalacewar da tsarin auren ya yi ne, da kuma yadda matan ke fargabar makomarsu a gidan miji, amma ta yarda da tasirin canjin zamani da kuma wayewar da mata su ke cigaba da samu a matsayin dalilan da suke samar da hakan.

A ganin wannan marubuciya, idan har mace ta san za ta iya tsare mutuncin kanta, aure bai zama wajibi a kanta ba, sai dai abin da ke zama matsala shi ne yadda al’umma ke kallon rayuwar ’ya mace idan har ba ta yi aure ta haihu ba, ko dai a riqa mata kallon ba ta cika mace ba, ko kuma a riqa yi mata zargin rashin tsare kai da halayyar banza. Domin kuwa matsalolin da ake ikirarin aure na karewa ko yana maganin su, kamar su zinace-zinace, samarwa ɗa asali da kuma kula da buƙatu da ɗawainiyar juna, har yanzu duk da auren da ake yi ba a magance su ba.

A cewar ta, “Zinace-zinace ba su ragu ba har a tsakanin masu aure maza da mata, yaran da ke girma gaban iyayen su ba su fi yaran da ba su da iyaye tarbiyya ko samun cigaban rayuwa ba, sannan mazaje da dama ba sa iya sauke nauyin iyali dake kansu, musamman ciyarwa da kula da sauran buƙatu na aure.”

Lura da yanayin halin da rayuwar aure ta samu kanta a ciki, a cewar Malama Rahama Abdulmajid shi ya sa mata suke jimawa ba su yi aure ba, saboda suna ƙoƙarin tantance irin mazajen da za su aura, gudun kar su yi ɗaukar kara da kiyashi.

Wannan ra’ayi nata ya samu goyon bayan wata ’yar kasuwa Malama Fatima Sayyida dake zaune a cikin garin Kano wacce kuma tana daga cikin matan da suke ganin rayuwar aure tana fuskantar tangarɗa, don haka lallai ne sai sun natsu kafin su fitar da mijin aure, wanda suke kyautata zaton zai riqe su da amana kuma ya kare mutuncin su, abin da suke ganin ya yi ƙaranci a zamantakewar aure ta yanzu.

Sannan kuma iyaye yanzu sun fi ba da muhimmaci ga bai wa ’ya’yansu mata ilimi mai zurfi, ta yadda za su shafe shekaru suna karatu daga sakandire zuwa jami’a har zuwa hidimar ƙasa, kafin daga bisani a fara tunanin aure. “Don haka sai ka ga mace ta daɗe a gida ba tare da ta yi aure ba, a lokacin da take buqatar auren kuma su ma mazan na ganin ta fi ƙarfinsu, saboda ta samu ilimi mai zurfi da wayewa, wani lokaci ma fiye da su mazan.”

Hajiya Maryam Ali Ali marubuciya kuma mai nazari kan al’amuran yau da kullum ita ma tana da wannan ra’ayin na cewa fifita karatu mai zurfi da ake yi kan aure yana taimakawa wajen daɗewar mata a gida ba tare da aure ba. A ganin ta aure da wuri ko haihuwa ba sa hana karatu, matuƙar kowanne ɓangare an ba shi haƙƙin da ya kamata a ba shi.

Tana mai cewa, “mu ma duk karatun da muka yi mun yi ne daga dakunan mazajen mu, kuma bai hana mu zaman aure ba, kula da hidimar gida kuma ba ta kawar da tunanin mu daga karatun da muke yi ba.”

A cewar Hajiya Maryam, idan da za a fitar da wani tsari na makarantun sakandire na matan aure zai taimaka wajen ƙarfafa gwiwar mazaje su goyi bayan karatun matan su, kuma hakan har wa yau zai rage zaman ’yan mata a gidajen su da sunan karatu.

“Saukaka yanayin samun ilimi da buɗe ƙofar neman sa ga kowa da kowa hanya ce da za a bi wajen yaƙar jahilcin da ke damun al’umma da samar da kyakkyawar fahimta a tsakanin maza da mata, ta yadda aure zai zama abin da kowa ke kwaɗayin samu yake kuma alfahari da shi, a maimakon fargabar abin da auren zai haifar wa mutum,” cewar marubuciya Rahama Abdulmajid.

A hasashen da Farfesa Fatima Umar ta Jami’ar Bayero dake Kano ta yi kuwa, wayewar zamani da aka samu ta yadda mata suke samun fahimta iri-iri daga karance-karancen litattafai zuwa bayanai da suke tattarowa daga yanar gizo, kallace-kallacen finafinai da sauransu na daga cikin abubuwan da suke buɗewa mata ido suna kallon yadda mata a wasu ƙasashen waje suke sarrafa rayuwarsu da zavar wa kawunan su abin da suke so shi ya sa suke ganin sai sun tantance abin da suke so su yi da rayuwarsu. lokacin da ya dace su yi aure, wanda ya dace su aura da kuma irin yanayin zaman da suke so su yi a gidajen su na aure. Sabanin yadda a shekarun baya inda mace ba ta da wannan ’yancin na sarrafa rayuwarta sai abin da aka zava mata.

A ganin Hajiya Uwa Idris marubuciya kuma jagoran wata ƙungiya mai zaman kanta dake Kaduna wacce ke taimakawa matasa da masu aure shawarwari game da zamantakewar iyali wato ‘Initiative for Counseling and Care’ wannan sabon canjin tunani da ’yanci da mata suka samu, sakamakon yaduwar ilimi da wayewar zamani ta sa su cikin wata dimuwa da yaudarar kai, suna ganin cewa, suna da duk abin da suke buqata, don haka ba lallai sai sun buqaci namiji ba. Kuma ko aure suka yi, namijinamiji ba zai juya rayuwarsu yadda yake so ba. Sakamakon abubuwan da suke kallo daga matan dake rayuwa a ƙasashen yammacin duniya.

Sannan kuma ta ce, su ma mazan yanzu lura da yanayin wayewa da bude idon da matan suka samu kan su a ciki ya sa suke tsoron tunkarar matan da sunan aure, suna fargabar matan ba za su yi musu biyayya ba, kuma ikon tafiyar da auren ba hannun su yake ba, sai yadda macen ta zaɓi a yi. Ba kamar yadda a shekarun baya iyaye da kakanin mu suka zauna zaman biyayya da bautar Ubangiji ba. Yanzu matasa ba sa yi wa aure kallon ibada sai dai wata hanya ta cimma muradin zuciya. Kuma daga mazan har matan ba wanda yake kallon dan uwansa a matsayin abokin neman tsira da gina ingantacciyar rayuwa, sai dai tunanin yaudarar juna ko amfani da wata dama don cimma wata manufa.

Za mu cigaba a mako mai zuwa…