Saƙo ga Musulmai daga Tiktok

Daga FATUHU MUSTAPHA

Na yi dogon rubutu na kammala a kan wannan bidiyo, amma sai na neme shi na rasa. Dole sai da na sake komawa tiktok na nemo bidiyo ɗin.

Ina ganin wannan bidiyo na kasa yana ishara ne da hadisin da aka ce Manzon Allah (SallalLahu alaihi wa sallam) ya faɗa ne, da yake cewa “…Dan Allah ku kula da mata”. A fahimtata ya danka su amana ne a hannunmu, amma ko shakka babu, wannan amana ta mata da ‘ya’ya da aka damƙa mana, ta tabbata da yawa daga cikinmu mun ci wannan amana.

Da farko dai, a jiya da dare na ci karo da wannan bidiyon a tiktok, na wata yarinya da ta kira kanta da suna, Rida Yakubu. Abinda ya kara tayar min da hankali shi ne, ta samu ‘likes’ sama da dubu sittin (60,000), da kuma comments sama da dubu biyu (2000). Ba wannan ne kawai abin tsoron ba, kurin da ta yi ta bayyanawa duniya halin da ake ciki, ya bai wa wasu yan matan musulmi damar su ma su fito su bayyana irin wannan halin da suka tsinci kansu. Inda suka tsunduma soyayya da samarin da ba musulmai ba. Hakan na ishara da cewa, lallai akwai wata a ƙasa. Domin kuwa na duba kwamen-kwamen da aka yi mata, na samu sama da ‘yammata Hausawa 600 da suka bayyana cewa su ma fa suna cikin irin wannan hali. A cikinsu mace ɗaya ce na ga ta nuna nadamar yin hakan saboda gudun ɓacin ran iyayenta. Wannan shi ne sakamakon wulaƙanta aure, sakin aure ba tare da wani dalili ba, da wulaƙanta mata da mazan Hausawa ke kallo a matsayin wata ƙasƙantacciyar halitta. Duk kuwa da da faɗar Allah na cewa: “Lallai na karrama dan Adam”. Amma sai Bahaushe ya sanya a ransa cewa, ana nufin mazan hausawa, amma matansu su ƙarata can, ba su a wannan karramawar.

A wurin Bahaushe, yana da dama ya auri duk wacce ya ga dama, ya kuma kore ta a duk yadda ya so. Zai iya korar mace da ‘ya’ya ya auro wata ya sanya ta a ɗakinta. Haƙƙin ‘ya’yan da ya haifa kuwa ko oho!

A wurin bahaushe, Allah bai daura masa wani nauyi na rayuwa ba, da ya wuce ya mace. Don haka a kullum, hanƙoransa na ya sauke wannan nauyi ne ko ta halin ƙaƙa.

A fahimtar addinin Bahaushe, zama da mace mai ilimi haɗari ne, macen da ta fita neman na kanta, neman maza take. ‘Yancin mace na ta bayyana ra’ayi ko ta bayyana kukanta saɓa wa Allah ne, domin a wurinsa, muryarta ma tsiraici ce.

A wurin Bahaushe musulmi, mace ba ta da wata ƙima da ta wuce ta ƙirar jikinta da Allah ya yi mata, sanda duk wannan ƙirar ta tawaya, walau dai sakamakon rashin lafiya ko tsufa, ko ma ta dalilinsa, to yana da damar ya kore ta ya nemo wata da ta dace da sha’awarsa ta jima’i ya kawo gida.

Haƙƙin da addini ya bai wa mace na ta nemi na kanta, kamar yadda muka gani a rayuwar Nana Khadija, da wasu mata sahabbai, ta nemi ilmi kamar yadda muka ji Manzon Allah (SallalLahu alaihi wa sallam) ya bayyana cewa “ku nemi rabin ilmin addinin ku a wurin Nana Aisha” hakkin ta na ta bayyana ra’ayinta, kamar yadda muka ji a rayuwar mata sahabbai, yau duk an kore wannan.

A saboda Bahaushe na kallon mace a matsayin wani nauyi, shi ya sa zai iya ɗaukar ta ya baiwa mutumin da ya tabbatar ba shi da garanti na wurin kwana, bai da tabbacin ciyar da ita ko tufatar da ita, balle a yi maganar ilmi. A haka za ka ga mutum a ɗakin haya, yana da mata da ‘ya’ya tara, kuma duk shekara sai ta haihu. Ka rasa ma ya ake ana kwanciyar sunnar!

Wani abu da na lura da shi, na bi yawancin yaran da ke da wannan matsala, na duba akwatin saƙonsu, na ga da yawan wallafe-wallafensu ma, suna nuna irin ƙaunar da suke wa addinin Musulunci, da yawan su suna nuna ƙaunar su ga Ƙur’ani. Wanda hakan ke nuna ba wai addinin ne ya takura su ba, halayyar mabiya addinin ce ta zamar wa rayuwarsu tarnaƙi. Ta hana su ‘yancinsu na rayuwa, ilmi, neman na kai, zamantakewa, zaɓi da sauransu.

Rida Yakubu, ɗaya ce daga cikin dubunnan mata musulmi dake arewacin Nijeriya da suka tsinci kansu a wannan hali, sakamakon halin ko in kula da suke fuskanta daga al’ummar da ya kamata a ce ta kare musu mutuncinsu da rayuwarsu, kamar yadda wanda aka aiko da addinin ya yi. Matuqar ba mu fahimci ginshiƙin zamantakewar aure a musulunci ya tattara ne a ƙarƙashin soyayya ba sha’awa ba, haka za ta cigaba da faruwa a cikinmu. Idan kunne ya ji, jiki ya tsira. Wannan ce ta sanya bango ya tsage, har kadangaru suka samu wurin shiga, lallai mu tashi mu yave wannan tsaga, in ba haka ba, da da daɗewa ba wannan tsaga za ta kayar da bangon gabaɗaya.

Rabbana la tuzigh ƙulubana, ba’ada iz hadaitana….

Allah ka tsare mana imaninmu.

Fatuhu Mustapha, marubuci ne, kuma mai sharhi a kan al’amurran yau da kullum. Ya rubuto ne daga Abuja.