Daga ABDULLAHI JIBRIL DANKANTOMA LARABI
Yau kwana uku babu wutar lantarki a Kano. Na yi amanna babu wani shugaba da zai kwana uku a gidansa ko ofis ɗinsa ba tare da wutar lantarki ba kuma ya ci gaba da rayuwa ‘normal’ irin yadda talaka ke rayuwa babu wuta. Shin malamai ba ku ba su labarin irin mulkin adalci da sahabbai suka yi ne? Sayyadina Umar (RA) ba ya iya barci face sai ya tabbatar da talakawan da yake mulki sun ci abinci sun ƙoshi kuma sun tabbatar da sun aminta da irin adalcin da ya ke yi musu.
Na taɓa karanta wani labari na King Fahad (Sarkin Makkah), inda ya ce, ya gode wa Allah da ya sa irin kalar abincin da mai mulki da kuɗi suke ci a Makkah irinsa talakawan garin Makkah suke ci. Duk wanda ya taɓa zuwa Saudiyya zai tabbatar da hakan ta yadda zai ga babu wani talaka da ya ke cin abinci babu nama kuma shinkafa dai Basmati wadda mai mulki da mai kuɗi zai ci ita dai talakan Saudiyya yake ci. Haka Laban Mara’i da mai kuɗi zai sha ko mai mulki shi talakan Saudiyya zai sha.
Amma a Nijeriya ba haka abin yake ba. Hatta wutar lantarkin a ƙasashen da suka cigaba an wuce wajen sama da shekaru 40 ba maganarta ake ba. Magana ake ta yadda za a bunƙasa harkokin ‘technology’ da bunƙasa harkokin kasuwanci da cigaban rayuwa yadda talaka zai amfana.
Tun da aka haife ni sama da shekaru 40 har yanzu a ce wai Nijeriya na fama da matsalar rashin wutar lantarki?
ƙasashen da basu kai mu cigaba ba ma a Afrika irinsu Nijar, Kwatano, Benin, Mali, Kongo. Kenya, Burkina Faso da sauransu; duk sun wuce matsalar wutar lantarki tunda idan ka je za ka ga suna da wuta awa 24.
Amma me ya ke faruwa da shugabanninmu na Nijeriya da ba za su samarwa da talaka wutar lantarki da ruwan sha da asibitoci masu kyau da hanyoyi masu kyau da makarantun gwamnati masu kyau ba? Ko iyakar waɗannan suka samarwa da talaka zai ji tabbas yana da shugabanni masu adalci da suke mulkar sa shekaru sama da 60 tun bayan da aka ba wa Nijeriya ’yancin kai. Shi ma zai tabbatar da cewar ya samu wani kaso cikin ‘yancin kan da ake tutiyar an samu shi ma ya mora.
Don Allah shugabannin Nijeriya kama tun daga kan shugaban ƙasa, gwamnoni, sanatoci, ’yan majalisun tarayya da na jihohi har zuwa kan ciyamomi da kansiloli, ya kamata ku zage damtse wajen ganin kun samar da hanyoyin da talakawan da ku ke mulka ko ku ke wakilta masu sauƙi da kuma inganta musu rayuwa.
Abdullahi Jibril Dankantoma Larabi ya runbuto ne daga Jihar Kano a Tarayyar Nijeriya
Alhamis, 9 ga Janairu, 2025