Sin: Ɓangaren Amurka ne ke yaɗa labaran bogi da ƙarairayi

Daga CMG HAUSA

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Zhao Lijian, ya musanta kalaman da jakadan Amurka dake ƙasar Sin R.Nicholas Burns ya yi game da rikicin ƙasashen Rasha da Ukraine da kuma dakin gwajin ƙwayoyin halittu na ƙasar Amurka dake Ukraine, yana mai jaddada cewa, jami’an Amurka ne, ba ƙasar Sin ba, wadanda suka riƙa yada labaran bogi da kuma yada ƙarairayi.

Zhao Lijian ya ce, ƙasar Sin a ko da yaushe tana yanke hukunci bisa gaskiya da adalci ta hanyar dogaro da shaidu na tarihi da ‘yanci kan batun Ukraine.

Akwai bayanai masu tarin yawa da hujjoji game da batun ɗakunan gwaje-gwajin nazarin ƙwayoyin halittu na Amurka dake ƙetare, ciki har da kafa guda ɗaya a ƙasar Ukraine. Al’ummomin kasa da ƙasa sun damu matuka game da wannan batu, kuma ƙasar Amurka na da alhakin yi wa duniya ƙarin bayani.

Fassarawar: Ibrahim