Da me a ke layya?

Da farko ina amfani da wannan dama domin mu tunatar da junanmu.

Layya dai ibada ce don haka tana da hukunce-hukunce tare da tanade-tanade, amma fahimtar hakan sai a wajen malamai masana.

Ɗan uwa, a Musulunci a kula, Layya ba a buƙatar a mallaki dabba ta hanyar haramun ko kuma a yi layya domin a burge ko a fusata jama’a.

Duk wanda ya kyautata niyya kuma ya yi aiki da ilimi, wannan ce hanyar dacewa. A yanzu za a samu ga namiji ya yi layya a tilascin matarsa ko kuma gasa ta abokai, duka hakan da matsala don haka hatta yawo da hotunan dabbobinmu da wasu ke yi akwai matsala ta fuskar addini.

Da fatan Allah ya yalwata mana, kuma ya azurta mu da yin ibada dominsa tare da dacewa.

Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa 07066434519-08080140820.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *