Sin: A ci gaba da daidaita yanayi a Ƙasar Mali

Daga CMG HAUSA

Dai Bing, muƙaddashin jakadan ƙasar Sin a MƊD, ya gabatar da jawabi a yayin taron kwamitin sulhun majalissar game da Mali, da ya gudana jiya Talata, inda ya yi kira da a ci gaba da ƙoƙarin daidaita yanayin da ake ciki a ƙasar Mali, musamman ma a fannin harkokin siyasa.

Mista Dai ya ce, zuwa yanzu an samu ci gaba a fannin shirin mika mulki, da yaƙi da ayyukan ta’addanci a ƙasar Mali.

Don haka, ya kamata a kiyaye wannan yanayi mai kyau da ake ciki, da ƙara ƙoƙarin wanzar da dauwamammen zaman lafiya da ci gaba a ƙasar.

Jami’in ya ƙara da cewa, ƙasar Sin na ɗora muhimmanci kan buƙatun ƙasar Mali a fannonin ikon mulkin kai, da tsaro, da raya ƙasa, kana tana goyon bayan al’ummar ƙasar da su zaɓi hanyar raya ƙasa da ta dace da yanayin ƙasarsu.

Jami’in na Sin ya bayyana cewa, ƙasar Sin na son samar da ƙarin taimako ga ƙasar Mali, a ƙoƙarinta na tabbatar da hadin kan ƙasa, da samun zaman lafiya da ci gaba.

Mai fassara: Bello Wang