Ilimin abinci abu ne mai wahala, dole sai an jure – Chef Khadija

“Don riƙa yin jagoranci na yin abincin mu ka kafa ƙungiya

Daga IBRAHIM HAMISU, Kano

Chef Khadija Idris Sulaiman ƙwararriya ce da ta ƙware wajen iya abinci da dukkanin nau’o’in snacks, baya ga haka, ita ce shugabar Ƙungiyar Mata masu saida Abinci ta Jihar Kano, wato Dexterity Food Forum. A hirarta da wakilinmu a Kano, Ibrahim Hamisu, za ku ji irin ɗimbin nasarorin da ta samu da kuma ƙoƙarin da suke na shirya taron cin abinci na mutum 600 a Kano. Ku biyo mu don karanta yadda tattaunawar za ta kasance:

BLUEPRINT MANHAJA: Masu karatunmu za su so ki gabatar da kanki?

CHEF KHADIJA: Sunana chef Khadija Idris Sulaiman, wacce aka fi sani da chef Khadija, an haife ni a unguwar Galadanci da ke cikin birnin Kano, ni ce mai gidan abinci na Deejerh Delicatedishes, sannan kuma ni ce na ƙirkiri ƙungiyar Dexterity Food Forum, wato Ƙungiyar Mata masu yin Abinci Nijeriya, mai shelkwata a Kano.

Ɓangaren karatu fa?

To na yi firamare a ‘Staff school’ Kano, daga nan na je garin Yola ta Jihar Adamawa, na yi aji ɗaya zuwa uku na sakandire. Daga nan na tafi FGGC Bakori na yi aji huɗu zuwa shida na sakandire. A rayuwar wannan makaranta na yi zama shugabar ɗalibai a lokacin da na ke makarantar, Ina gama sakandire na yi JAMB inda na cike Jami’ar Bayero, aka bani ‘Biochemistry’. Na yi, na kuma kammala a 2019, kafin na yi bautar ƙasa. Yanzu haka Ina da aure da ɗa ɗaya.

Da wacce sana’a kika fara?

To da farko na fara sana’a ne tun a shekarar 2019, ganin cewa Ina zauni ba ni da sana’a na ga ba lallai ba ne aiki ya samu ba, sai na ga ya kamata na fara sana’a, to a lokacin na fara da kayan fulawa ne, idan na yi a cinye, to sai na ga mai zai hana na fara fitarwa shagon gidan da na ke aure, to na fara Ina kaiwa kamar guda 20, wata rana ya qare, wata rana ya kwana biyu bai ƙare ba, har na zo Ina fita taro.

Ko za ki lissafa mana abubuwan da kike sayarwa?

Abubuwan da mu ke yi su ne Snacks; Samosa, spring rool da duk wani nau’in kayan fulawa. Ina kuma yin wasu daga cikin nau’ukan abinci da yawa.

Wasu daga cikin ayyukan Khadija

Ke kasance shugabar ƙungiyar ‘Chefs Dexterity Food Forum. Ta yaya aka samar da wannan ƙungiyar?

Ƙungiya ce ta mata zalla masu sayar da abinci, wanda asali mun fara ne ta buɗe group ta Whastapp, sai mu ka fara shirya taro mu ka ga juna, sannu a hankali yanzu mu na da membobi fiye 300 a Jihar Kano, sannan mu na da membobi a jahohi goma na Arewa a yanzu.

Menene manufar ƙungiyar?

Manufarmu shi ne; mu taimaka wa na ƙasa su miƙe, na biyu shi ne, koyar da su ilimin sana’ar abinci, domin ilimin abinci abu ne mai ɗan wahala dole sai an jure, idan mutum bai dage ba, nan da nan zai haƙura, ya ce, ya gaji, na uku shi ne, mu riƙa yin jagoranci na yin abincin, misali, wata tana yin wani abinci, amma ba daɗi ba a saye, to za ta turo a group, sai mu zauna mu ga ta ina yake samun matsala ? Sai mu zauna mu bata shawara akan abinda ya kamata ta yi, sai ka ga an gyara kuma an samu nasara.

Su wane ne a cikin ƙungiyar?

Ƙungiyar ta kowa da kowa ce matuƙar mace ce, kama daga ‘yanmata, matan aure, tsofaffi, zawarawa da duk wata mai yin abinci ko na sha tana iya kasancewa a cikin mu, akwai masu ma a cikin mu da makarantar koyar da abinci suke da ita, akwai kuma waɗanda ma ba su ma fara sana’ar abincin ba duk suna cikin mu.

Waɗanne irin nasarori za a iya cewa kin samu daga shekara uku zuwa yanzu?

Gaskiya alhamdu lillah. Na yi nasara, domin na fara yin ‘snarck’ guda 20 ne na ke bayarwa a shagon gidan da na ke aure, ko asiyar ko a yi kwantai, har aka kai odar ta fi ƙarfin gida, na fara fita taro, daga nan sai na buɗe babban wuri a gaban gidana, kuma alhamdu lillahi a lokacin na fara fitar da Samosa guda 20, amma a yanzu mu na fitar da 5000 a sati, idan akwai taro mu na fitar da fiye da haka. Sannan wannan ƙungiya ta samu nasarar buɗe reshe a jahohi goma na arewacin Nijeriya, kuma nan gaba mu ke fatan ta karaɗe dukkanin Nijeriya.

Daga cikin nasarorin akwai mata goma na wannan ƙungiyar da mu ka samu yi wa NGO kwangilar yin abinci na kwana shida, inda mu ka rarraba su cikin ƙauyukan Kano. Sannan kuma wannan ƙungiyar ta shirya taro da CAC da NAFDAC da FIRS a gidan marigayi Bashir Tofa, mu ka sa ‘yan ƙungiya siyo girki mu ka ɗanɗana masu gyara aka gyara masu.

Domin a kullum mu na gayawa membobinmu cewa, kafin ki fara sana’a yana da kyau ki yi rijista da waɗannan hukomin da na ambata, domin ko kasuwanci za ka yi da mutum idan ya ga sunan kamfaninka zai fi gamsuwa akan ya ga sunanka, a qarshen shekara sai aka tara gabaɗaya ‘yan wannan ƙungiya akai masu bita, sannan aka rarraba ɓangare-ɓangare aka ce kowacce ta tafi ɓangare ɗaya ta tabbatar ta ƙware a ɓangaren.

Haka kuma na zo ta biyu a gasar girki ta Maggi a cikin shekarar da mu ke ciki, inda na rabauta da kyautar miliyan ɗaya, In taqaice ma ka yanzu a ƙasa da shekara uku na yi nasarar da wanda ya shekara goma bai samu ba. Alhamdu lillahi.

Ƙalubale fa akwai ko babu?

Ƙalubale ba zai wuce waɗanda suke a wajen Kano ba, akwai wasu da suke ganin ya za a yi ace ni da ba gari ɗaya mu ke ba, amma na shugabance su, to shi ne suke fita suna kafa ta su ƙungiyar, to shi ne dai ƙalubalan, amma anan Kano suna ba mu haɗin kai ɗari bisa ɗari.

Za ku yi taro a ranar 16 ga watan da mu ke ciki na Oktoba. Menene maƙasudin taron?

To kasan na gaya ma akwai NGO da suka ba mu kwangilar yin abinci, to sai suka tambaye mu ana ba mu takardar girmamawa na ayyukan da mu ke yi? Sai mu ka ga yawanci ba mu da shi.

To sai mu ka ga yakamata mu shirya taron bada takardar girmamawa mu bai wa wasu daga cikin mu da suka ƙware a fannoni daban-dadan, to shi ne mu ka maida shi babban taro, inda za mu ɗauko manya a cikin ‘industry’ na abinci da suka bada gudunmawa a cikin al’umma kamar masu gidan abinci, masu sayarwa akan hanya da kuma mu ‘yan ƙungiyar, mu karrama su. Za mu taru, za a ci a sha.

Tabbas za a ci abinci kala-kala, wanda daga wannan duk shekara za mu riƙa yi, kuma mun zaɓi ranar 16 ga watan Oktoba ne, saboda ita ce ‘International Chef Day, wato ranar Abinci ta Duniya, inda mu ke sa ran mutum 600 za su halarta, a nan cikin birnin Kano.

Farkon sunanki ana sa Chef. Me chef ke nufi?

Chef shi ne wani babban matsayi ne na masu saida abinci, duk wanda ka gani to babba ne, wanda ya san mai yake a harkar saida abinci. Misali, idan ya ɗaga tumaturi, ba wai kawai ya yi girki da shi ba, a’a ya san me ya sa yake amfani da tumaturi, saboda ya karanta ne ba kara zube yake yi ba.

Kuna da chef da yawa ne a cikin ku?

Eh, mu na da yawa daidai gwargwado, domin kasan na gaya ma ka cewa, a cikin mu a kwai masu makarantun koyar da abinci. Don haka idan mutum yana son zama zai iya yin rijista, zai iya kwashe wata biyu yana zuwa ana koya masa. Zai koyi girki kala-kala, sannan sai a ba shi takardar shaidar zama chef wato ƙwararre a harkar abinci.

Me ake sa ran gabatarwa a wajen wannan taro?

Za a gabatar da lakca, kasan na gaya ma ka a shekarar da ta gabata mun yi taron shekara-shekara, amma kasan ba komai mu ka yi ba, don haka a wannan karon za a yi lacka ne akan tattalin sana’a, domin da yawa za ka ga an fara sana’ar, to, amma rashin yadda za a yi tattalin sana’ar ta ɗore shi ne abinda mu ke fama da shi a mutanenmu, don haka duk wanda ya je wajen taron zai ƙaru da wannan Ilimin.

Yan Kungiyar Dexterity Food

Yaya za a yi mutum ya halarci wannan taron da za a yi 16 ga Oktoban da mu ke ciki?

Eh ticket mu ke sayarwa, duk mutum ɗaya zai sayi ticket 5,000, kuma sannan za mu bai wa kusan duk wanda yaje wurin musamman ma manyan mutanen za mu ba su takardar shaida (certificate) domin shi kansa takardar shaidar zai qara wa mutum qima da daraja, kuma za mu haɗu da manyan mutane, mu kuma gana da kwastomomi, sannan a yi ‘Networking’ da sauran su.

Menene kiran ki ga ‘yan ƙungiya da sauran al’umma?

Kirana ga ‘yan ƙungiya shi ne, lallai su yi ƙoƙari su yi rijista kafin 16 ga watan da mu ke ciki, musamman masu yin abinci, domin rana ce ta musamman da za a yi nishaɗi kuma rana ce da za a ci a sha, domin aƙalla za a ci a sha kamar kala bakwai, kuma kala bakwai ɗin sai ka zavi wanda kake so, tun daga shigar mutum ɗakin taron kana zama za a fara ba ka abin tava wa daga nan har a tashi. Su kuma al’umma mu na kira gare su da su zo su yi rijistar don su taya mu murna wannan rana ta masu abinci ta duniya.

Na a gode

Ni ma na gode ƙwarai