Sin da Argentina sun sha alwashin yayata manufar samar da al’umma mai makomar baiɗaya

Daga CMG HAUSA

Yayin da ake bukukuwan cika shekaru 50 da kafuwar dangantakar diflomasiyya tsakanin Sin da Argentina, a jiya Laraba, an gudanar da babban dandalin musayar al’adu tsakanin sassan biyu a nan birnin Beijing, inda a yayin zaman, manyan jami’ai daga ƙasashen biyu suka sha alwashin ci gaba da ingiza manufar nan ta samar da al’ummar duniya mai makomar bai daya ga ɗaukacin bil adama.

Sama da wakilai 100 daga tsagin Sin da na ƙasar Argentina ne suka halarci dandalin, wanda kafar CMG da gungun kafofin yada labarai na Argentina suka dauki nauyin shiryawa.

Kaza lika dandalin ya kasance ɗaya daga ayyuka daban daban, na yauƙaƙa kawancen ƙasashen biyu da aka shirya gudanarwa a shekarar nan ta 2022.

Mai fassarawa: Saminu Alhassan