Sin ta ƙalubalanci ƙasashen Yammacin duniya da su tuna da laifinsu na mulkin mallaka

Daga CMG HAUSA

Mataimakin wakilin Sin dake ofishin MƊD da sauran ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa na birnin Geneva Li Song ya yi jawabi a gun taron tattaunawa kan tasirin da mulkin mallaka ke yi wa haƙƙin ɗan Adam, wanda aka yi a taron majalisar kare haƙƙin ɗan Adam ta MƊD karo na 51, inda ya ƙalubalanci ƙasashen yammacin duniya ciki har da Amurka da Birtaniya da sauransu, da su tuna da laifinsu na mulkin mallaka da kuma ɗaukar matakai don gyara kuskurensu.

Li Song ya yi nuni da cewa, a halin yanzu da ake bin tsarin demokuraɗiyya a hulɗar ƙasa da ƙasa, bai kamata wata ƙasa ta nuna ƙarfi kan sauran ƙasashe ba.

Ya ce har yanzu, waɗancan ƙasashen da suka taba yin mulkin mallaka, sun kira kansu masu rajin kare haƙƙin ɗan Adam.

Don haka, Sin na ƙalubalantar ƙasashen da su yi watsi da tsoma baki cikin harkokin cikin gidan sauran ƙasashe, da kuma daina siyasantar da batun kare haƙƙin ɗan Adam.

Li Song ya ƙara da cewa, bisa yanayin tinkarar cutar COVID-19, ya kamata ƙasashen da suka ci gaba, su ɗauki matakai a fanonin rage basussuka da samar da gudummawar raya ƙasa don taimakawa ƙasashen da suka taba yi musu mulkin mallaka su samu ci gaba.

Mai fassara: Zainab