Gwamnati ta ayyana Litinin mai zuwa ranar hutu don bikin samun ‘yancin kan ƙasa

Daga BASHIR ISAH

Gawamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin, 3 ga Oktoban 2022, a matsayin ranar hutu don bikin cikar Nijeriya shekara 62 da samun ‘yancin kai.

Bayanin hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar da Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, ya fitar a ranar Laraba mai ɗauke da sa hannun Babban Sakataren Ma’aikatar, Shuaib Belgore.

Minista Aregbesola ya yi amfani da wannan dama wajen taya ‘yan ƙasa murnar bikin, ya kuma ba su tabbacin gwamnati za ta ci gaba da yin bakin ƙoƙarinta wajen shawo kan matsalolin da suka addabi kasa tare da kyautata rayuwar al’umma.

Ya ce, “Duniya na fuskantar ƙalubalen tattalin arziki da na tsaro wanda hakan ya shafi ƙasarmu.

“Ina mai ba ku tabbacin gwamnati ba za ta yi watsi da ‘yan ƙasa ba, za ta ci gaba da jajircewa wajen tunkarar matsalolin har sai ta ga bayansu.”

Daga nan Ministan ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi nazarin matsalolin da suka addabi ƙasa sannan kowa ya duba ya ga irin gudunmawar da zai iya bayarwa domin magance su.