Martani da amsoshin sharhin da Bamai Dabuwa ya yi, a kan littafin ‘Asalin Labarina’

Daga AYUBA MUHAMMAD DANZAKI

Da farko zan soma da yabo da godiya da shi wannan zaƙaƙurin marubuci ya yi. Hakika na ji daɗi sosai yadda ya vata lokaci wajen karanta littafin da farko har ƙarshe, sannan ya kawo min gyare gyaren da ya yi hasashen cewa kura-kurai ne.

(1) Da farko zan fara da ƙa’idojin rubutu ina ganin ko kilu ta kila mai ganin man dutse ne ya duba ƙa’idojin rubutun nan dole ya yaba don an yi ƙoƙari ba ɗan kaɗan ba, duba da wanda ya yi typing ɗinsa tun daga farko har ƙarshe, yabo a kan ƙa’idojin rubutu ya fi yawa akan gazawarsa.

(2) A game da maganar sanya kalmar turanci a cikin baka, tabbas wannan kuskure ne amma ba kai tsaye ba, kasancewar duk kalmar da aka sanya a baka ana son nuna mahimmacin abu ne ko haskaka shi a gane wannan abin aro ne ko kambamawa.

(3) A game da maimaicin kalmomin wannan kuskure ne, amma kuma wani abin, abin birgewa ne ka kawo kalmomi masu ma’ana daban-dabam wanda bai sani ba, kamar misali da ka kawo cewa yana da kyauta da kyautatawa, ina ganin wannan ma adonta harshe ne.

(4) Misalin da na kawo inda nake cewa da yake lokacin, lokaci ne na damina (raining season) abin da na so Malam mai sharhi ya gane, shi fa yaren Hausa ba wai iya Hausawa ne suke amfani da shi ba, akwai yararruka da yawa da suke koyon Hausa ciki har da Turawa, Yarabawa, don ka ce musu damina lokacin damina kai tsaye bai zama lallai su gane kai tsaye ba, amma idan ka kawo na Hausan ka fassara shi da Turanci tamkar ka ba su sauƙi ne wajen fahimtar da su abin da Hausar take nufi ne.

(6) A game da kalmar Metron Suwaiba, kalmar metro ita ce daidai, amma ka sani ita matar da na kawo a labarin akwai ta a gaske ba wai ƙirƙirar sunan na yi ba, sanda na rubuta labarin shekaru kusan ashirin ba ya aikinta ke nan kuma sunanta ke nan Metron Suwaiba har gobe haka ake cewa da ita duk da ta yi retire ma yanzu haka a aikin ko yanzu ka buƙaci ganin ta ka zo na kai ka ku gaisa sunanta kenan Metron Suwaiba.

(5) Kufcewar Salo tabbas wannan kuskure ne ni ma na fahimci hakan saboda babu yadda za a yi jariri ya ba da labarin sanda aka haife shi, da kaina na kirawo wani marubuci takwaranmu sanda na ji an karanta gurin a gidan radio kai tsaye na karɓi wannan gyaran.

(7) Karin magana ko azancin magana ba dole ne don za ka rubuta ƙagaggen labari ba a ce dole sai ka kawo karin magana matuƙar jigon da kake kai ya ba da ma’ana babu buƙatar karin magana, amma dai yana armasa labari kuma ina yawan kawo karin magana a sauran littattafaina je ka ka karanta littafina ‘Rayuwar Bilkisu’ a nan za ka ji karin magana kamar jaka a kano.

(8) Kalmar qarya a labarin, ka fahimceni wani abu wannan ba zai zama kuskure ba, duk wadda take zuwa awo Asibitin Malam Aminu Kano tsakanin 2004 zuwa 2005 ƙarya ta ke yi ta ce Metron Suwaiba ba ta taimake ta ba ka je ka bincika gaske ne ba kawai ƙirƙira ba ce.

(9) A game da zancen ‘yar aikin gida, zan so mai sharhi ya je ya bincika sosai gidajen masu kuɗi da suke ɗaukar ‘yar aiki ba ko yaushe ne suke barin ‘yar aiki ta girka musu abin da za su ci ba, akwai abin da dole matar gida ita take dafa kayanta ba tare da ‘yar aiki ba, ashe kuwa ba lallai ba ne don Larai tana matsayin yar aiki a gidan Alhaji Rabi’u an samu wani lokaci Hajiya Aisha mahaifiyar Ziya ta yi girki da kanta.

(10) Alaƙar suna da bangon labarin na so a ce ka san ina ne garin Zainawa ko ka tava zuwa da ka gaskata ni wajen kawo hoton buzaye da wannan raƙuman da kai da kanka za ka san ba wai shaci faɗi aka yi ba, ko yau ka doshi garin Zainawa farkon shiga garin abin da za ka fara yin tozali da shi ke nan, buzaye da raquma da kyawawan gidaje ginin ‘yan birni da na mutanen karkara.

(11) Wai kai baka san ana haɗa soyayyen dankali na turawa a haɗa da soyayyen kwai a sha shayi da shi ba, Lallai da sauranka. Anya kana mu’amula da ‘yan birni kuwa? Hahaha!

(12) Bincike game da labari ko ba a gaya maka ba ka san an yi bincike sosai yayin rubuta littafin ‘Asalin Labarina’ tun da aka ɗauki cutar HIV kuma aka fita waje a nemo maganinta ka san ba wai an yi daki da ka ba ne.

(13) Kalmar tarin tv zan tuntuɓi wani abokina likita Doctor Rabbilu Sale Danzaki, yadda muka tattauna zan zo maka da cikakken bayani ka ji.

A ƙarshe tausayi bai zama jigon ‘Asalin Labarina’ ba, illa an gina labarin akan butulci da cin amana, don haka ban ga laifi ba, don daskararriyar zuciyarka mai kama da kankara ta ki tausayawa jarumin littafin Ziya’u ba,

Kawai dai dadin da na ji da na kawo tsohon labari aƙalla shekaru ashirin da rubutunsa ya dawo a wannan zamanin yake gogayya da rubutun wannan zamanin da gwanayen na iya suka fi ganin sun fi kowa iya salo da sarrafa harshe.

Kullum burina in yi ta kawo ragon salo a labaraina matuƙar ba za suyi kamanceceniya da salon ko wanne marubuci ba, ballantana ya yi zaton an kwaikwaye shi ko kuma an yi masa satar fasaha ba.

Da fatan Malam mai sharhi kasance duk sanda ni Zakin Marubuta na fitar da sabon littafi shi ne zai kasance mai yi min sharhi.

Na gode sosai.
Marubuci Ayuba Muhammad Danzaki.
08067061458

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *