Mai garin Lakwaja, Alhaji Muhammad Kabir Maikarfi III ya rasu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Allah Ya yi wa Mai Garin Lakwaja, Alhaji Muhammad Kabir Maikarfi III, rasuwa yana da shekara 80 a duniya.

Masarautar Lakwaja, ta sanar da rasuwar Babban basaraken, wanda shi ne Shugaban Majalisar Masarautar ta ce, ya rsu ne bayan rashin lafiya a wani asibiti mai zaman kansa a Abuja.

Sanarwar da Sakataren Masarautar Lakwaja, Muhammed Nalado Usman, ya fitar a ranar Laraba da dare ta ce za a yi jana’izar basaraken ne da misalin ƙarfe 4 a ranar Alhamis a garin Lakwaja.

Alhaji Muhammad Kabir Maikarfi III ya rasu ne bayan shekara 30 a kan sarautar Mai Garin Lakwaja, wanda ya samu tun a shekarar 1992.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *