Siyasar Kano: APC ta dawo daga rakiyar Shekarau a rikicinsa da Ganduje?

*Shekarau ya yi watsi da ƙa’idojin sulhun Buni
*Ganduje da mabiyansa sun goce da murna
*Hukuncin kotu na cigaba da zama tarnaƙi

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Tataɓurza da rikicin shugabancin jam’iyyar APC a Kano na ƙara ɗaukar sabon salo bayan uwar jam’iyyar ta ƙasa ta fito da ƙa’idojin sulhu, don sasanta ɓangaren da Sanata Ibrahim Shekarau ke jagoranta da kuma na Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, inda ɓangaren Malam Shekarau ya yi watsi da sanarwar uwar jam’iyya kan sulhunta rikicin ‘ya’yanta na jihar.

Gabanin hakan dai, ɓangaren Shekarau, wanda ya ƙunshi sanatocin jihar biyu da wasu manyan ’yan Majalisar Wakilai da wasu masu faɗa a ji a siyasance, sun samu nasarori guda biyu, wato a ɓangaren kotu da kuma ita uwar jam’iyyar, wacce tun da fari ita ce ta amince da zaɓukan jam’iyyar, wanda tsagin Shekarau ya gudanar.

Tsagin Sanata Shekarau dai ya zaɓi Alhaji Haruna Ɗanzago a matsayin shugaban jam’iyyar a Jihar Kano, wanda hakan ke nufin hana Gwamna Ganduje jagorancin jam’iyyar, saɓanin al’adar Jam’iyyar APC da aka sani tun kafa ta.

To, amma bayan zaman sasanci ya ci tura a tsakaninsu a Abuja a makon jiya, inda ta kai ga rantsar da shugabannin jam’iyyar na jihohi a hedikwatarta da ke Abuja ba tare da Kano ba, sai uwar jam’iyyar a ƙarƙashin jagorancin shugabanta na riƙo suka yanke shawarar fito da ƙa’idojin sulhunta ɓangarorin, wanda kuma ɓangaren Malam Shekarau ke kallo a matsayin bai dace da muradunsu ba, domin tsarin ya nuna cewa, dukkan naɗe-naɗen kwamishinoni da masu bai wa gwamna shawara da masu taimaka masa na musamman da sauran zaɓaɓɓun jam’iyyar su ke da alhakin riqe ragamar jam’iyyar, sannan kuma shi gwamnan ne zai zama jagoran dukkan sabon tsarin da za a yi, kodayake tare da tuntuɓar Shekarau zai yi hakan.

Hakan ya nuna cewa, mafi yawan masu ruwa da tsakin da ke da ikon yanke hukunci a jam’iyyar za su kasance mabiyan Gwamna Ganduje ne, lamarin da zai hamɓarar da ikon ɓangaren Shekarau a dabarance kenan, kamar yadda suka zarga.

A takardar da sanatan mai Wakiltar Kano ta Tsakiya ya aike wa uwar jam’iyyar tare da sa hannun jiga-jigan tafiyar tasa, ya ce, sun yi watsi da wannan sanarwa kuma ba su amince da ita ba.

”Matsayinmu a kan wannan sanarwa matakai ne kamar guda uku: a duk zaman da muka yi kamar sau biyu ko sau uku, wanda Mai Girma Gwamna Ganduje ya na wurin da muƙarrabansa da waɗanda mu ma muka je tare da su, ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyyar Gwamnan Jihar Yobe Maimala Buni, an nemi kowane ɓangare ya bayyana matsayarsa da abin da suke son a yi da shawarar waraka kan wannan matsala. Duka mun bayar da namu.

Shugaban jam’iyya ya ce, za su koma su kalli bayanan da duka muka yi, domin fito da wata maatsaya da shawarar abin da ya dace a yi,” inji tsohon gwamnan na Kano a wata kafar yaɗa labarai.

Sanata Shekarau ya ƙara da cewa, sanarwar da jam’iyyar APC ta fitar ba ta yi magana a kan matsayar da aka cimma tsakanin ɓangarorin biyu ba, sannan jam’iyya ba ta faɗi komai tsakanin abin da ɓangarorin biyu suka buƙata ba.

“Abu na biyu, kafin a kawo takardar a matsayin wanda ya ke jagorantar ɗaya ɓangaren, sai da aka kai wa Gwamna Ganduje takardar, wacce kamata ya yi ta zama tsakanin shugaban jam’iyyar ko hedikwatar jam’iyya da gwamna da kuma ni shugaban ɗayan ɓarin jam’iyyar,” inji Shekarau.

Sannan ya ci gaba da cewa, kafin su samu takardar ta riga ta shiga duniya tana yawo a shafukan sada zumunta, yana mai cewa, “yaran gwamna na cewa an damƙa wa gwamna jam’iyya, ai ta koma hannunsa da maganganu makamantan haka.

“Abu na uku shi ne, yaya mutane biyu su na jayayya, sai kuma a ce ɗaya daga cikin waɗanda ake jayayya da shi ne zai jagoranci sasantawar, alhalin shi ya jagoranci waccan sasantawar da ba a yi mana adalci ba, da muke ganin an zalunce mu, ta yaya za a yi mana adalci a yanzu?

“Kamata ya yi uwar jam’iyya ta wakilta wanda zai jagoranci wannan zama. Don haka ba mu amince da shi ba, mun yi fatali da shi, ba mu yarda ba, ba kuma za mu amince ba. A ƙarshen takardarmu mun faɗa wa uwar jam’iyya mu masu biyayya ne, a shirye muke a sake zama, domin sasantawa.”

Shekarau ya ce, wannan dalili ya sa suka rubuta takarda suka aika wa shugaban jam’iyya, za kuma su bai wa ‘yan jarida da shafukan sada zumunta cewa abin da suka yi tsammani a yi ba shi aka yi ba.

A daren Litinin ne uwar jam’iyyar ta fitar da sanarwa kan yadda za a shawo kan matsalarsu da magance ta. Ta kafa kwamitin mutum biyar domin warware rikicin shugabanci da ya qi ci ya ƙi cinyewa a Jihar Kano tsakanin ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau da na Gwamna Abdullahi Umar Ganduje. Jam’iyyar ta sanya Gwamna Ganduje a matsayin shugaban kwamitin, sai kuma Sanata Malam Ibrahim Shekarau a matsayin mataimakinsa.

Dukkan mutanen biyu dai na ja-in-ja kan shugabancin jam’iyyar APC a jihar ta Kano, lamarin da ya janyo takun saƙa da sanya jam’iyyar cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi a jihar. Sauran ‘yan kwamitin akwai Gwamnan Jihar Zamfara Bello Muhammad Matawalle, da tsohon Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara, da Sanata Abba Ali, da kuma wakilin jam’iyyar da ake sa ran za a yi zama da shi.

Sanarwar ta kuma ci gaba da cewa, ana san kwamitin zai yi zama a Jihar Kano cikin kwanaki bakwai tare da miƙa wa jam’iyyar rahoto.

Sannan ta na fatan bai wa Gwamna Ganduje shugabancin kwamitin a matsayinsa na kamar Jagoran Jam’iyyar APC a Jihar Kano zai nuna kyakkyawan shugabanci a zaman da za a yi. APC ta ce, an ɗauki matakin ne saboda kotu ta gagara warware rikicin, alhalin dukkan ɓangarorin biyu ba za su kai labari ba a lokacin zaɓe, dole sai da ɗan uwansa.

Sanarwar ta qara da cewa, domin samun warware matsalar da samun jam’iyya guda ba ƙumbiya-ƙumbiya a jihar, ya na da matuƙar muhimmanci Gwamna Ganduje ya jagoranci kwamitin. Haka kuma, adalcin a nan ba wai rarraba madafun iko na jam’iyyar kaɗai ba ne, har da yi wa sauran ‘yan jam’iyyar adalci ta fuskar shugabanci.

Jihar Kano dai babbar jiha ce da APC ta daɗe tana nanata tasirinta a siyasar Nijeriya, abin da ya sa APC ɗin ke ƙara ƙoƙari wajen ganin ta hana wannan ɓaraka da ta kunno kai a jihar ƙara tsawo da faɗi.

Idan aka gaggara masalaha tun da wuri, babu mamaki wannan rikici ya kassara tasirin da APC za ta iya yi nan gaba, musamman a zaɓen 2023, kamar yadda ya faru a Jihar Zamfara ga APC lokacin zaɓen 2019, inda bayan kammala zaɓe, Kotun Qoli ta soke dukkan zaɓukan da APC ta lashe, ta miƙa wa PDP, wacce ita ce ta zo na biyu a zaɓen jihar, saboda ayyana APC da kotun ta yi a matsayin wacce ba ta bi ƙa’idoji wajen tsayar da ’yan takararta ba.

Duk da ya ke ‘ya’yan jami’iyyar a Jihar Kano na da ƙwarin-gwiwar sulhu zai tabbatu a tsakaninsu, amma masu lura da al’amuran yau da kullum na ganin cewa, za a kai ruwa rana kafin ya kasance an sasanta wannan rikici da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a jihar ta Kano, idan aka yi la’akari da buƙatun siyasa da suka dabaibaye siyasar Kano a matakin jihar da ma ƙasa bakiɗaya, saboda yawan guraben wakilai (delegates) da jihar ke da shi a Babban Taron Jam’iyyar na Ƙasa, wanda a ke sa ran gudanar da shi a ƙarshen watan Fabrairu.

Wannan saɓani dai ya fara jefa shakku kan ko dai uwar jam’iyyar ta dawo daga rakiyar Sanata Shekarau da magoya bayansa ne, inda za ta koma tsarinta na asali, wanda ya miƙa wa gwamnoni ragamar wuƙa da nama na jam’iyyar a kowacce jiha? Lokaci ne zai tabbatar da gaskiyar magana!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *