An yi jana’izar Magajin Garin Sakkwato, Hassan Danbaba

Allah Ya yi wa Magajin Garin Sakkwato, Alhaji Hassan Ahmad Danbaba, rasuwa.

Wata majiya ta kusa da ahalin marigayin ta ce, marigayin ya rasu ne ran Asabar a Kaduna bayan fama da rashin lafiya.

Dangi, ‘yan’uwa da abokan arziki na kusa da nesa sun bayyana rasuwar marigayin a matsayin babban rashi ba ga jihar Sakkwato kaɗai ba har ma da ƙasa baki ɗaya.

Tuni dai aka gudanar da jana’izar marigayin a Sakkwato daidai da karantarwar addinin Islama.